Jiragen Yakin Sojojin Sama Sun Kashe 'Yan Ta'adda da Dama bayan Yi Musu Ruwan Wuta a Jihohin Arewa 3
- Dakarun sojojin saman Najeriya na ci gaba da kokarin kawo karshen 'yan ta'adda da ke kai hare-hare kan bayin Allah
- Sojojin sun yi nasarar kai hare-hare a jihar Borno da wasu jihohin Arewacin Najeriya inda suka hallaka 'yan ta'adda masu yawa
- Hare-haren sun kara nuna kokarin da hukumomin tsaro ke yi domin kawo karshen matsalar ta'addanci a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hare-haren jiragen yaki na rundunar sojin saman Najeriya (NAF) sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP da dama a yankunan Mallam Fatori da Shuwaram na jihar Borno.
Hakazalika, hare-haren sojojin saman sun lalata sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Kwara da Katsina.

Source: Getty Images
Mai magana da yawun rundunar NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban 2025, cewar rahoton jaridar The Nation.
Sojojin sama sun kashe 'yan ta'addan ISWAP
Ehimen Ejodame ya bayyana cewa an gudanar hare-haren ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Nuwamba 2025, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Sanarwar ta bayyana cewa hare-haren, wanda aka gudanar da su bisa sahihan bayanan sirri, sun yi gagarumar illa ga ‘yan ta’addan ISWAP da ke yankin Arewacin Tumbuns.
“Jiragen yaki sun kai hare-hare a Kudu maso gabashin Shuwaram kafin su koma Mallam Fatori, inda aka hango ‘yan ISWAP suna taruwa kan babura da kwale-kwale a yankin Tafkin Chadi."
“Hare-haren sun lalata mafakar ‘yan ta’adda, wuraren ajiye kayayyaki, da wuraren adana makamai, tare da hallaka ‘yan ta’adda da dama da kuma toshe hanyoyin da suke bi."
"Binciken bayan hari ya tabbatar da kashe ‘yan ta’adda da dama da kuma raunana hanyoyin ayyukan ISWAP a yankin.”
- Ehimen Ejodame
An ragargaji 'yan bindiga
Sanarwar ta kara da cewa yayin da hare-haren ke gudana a Arewa maso Gabas, jiragen NAF sun kuma kai hare-haren sama a Garin Dandi da Chigogo a jihar Kwara, inda suka tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan
Kebbi: Mataimakin shugaban majalisa ya kubuta daga hannun 'yan bindiga, an ji yadda ya tsira
“Bisa sahihan bayanan sirri, hare-haren sun janyo firgici tare da haddasa asarar rayuka masu yawa ga miyagun."
- Ehimen Ejodame

Source: Facebook
A wani hari makamancin haka, jiragen yaki a karkashin rundunar Operation Fansan Yamma sun kai farmaki a tsaunin Zango da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda ke zama mafakar wani babban kwamandan ‘yan ta’adda da mayakansa.
An lalata wuraren ajiye kayayyakinsu da kashe ‘yan ta’adda da dama, a yayin harin wanda rundunar NAF ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin mafi nasara a yankin Arewa maso Yamma a ‘yan watannin nan.
Shugaban sojan sama ya sha alwashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon babban hafsan rundunar sojojin saman Najeriya, ya yi bayani kan irin salon jagorancinsa.
Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya yi alkawarin jagorantar runduna mai fasaha, ladabi, da kwarewa.
Sabon hafsan sojojin saman ya bayyana cewa rundunar da zai jagoranta za ta hana ‘yan ta’adda damar samun lokacin shirya kai hare-hare.
Asali: Legit.ng
