Illar Barazanar Trump: 'Yan Kasuwa a Najeriya Sun Yi Asarar Naira Tiriliyan 2.83

Illar Barazanar Trump: 'Yan Kasuwa a Najeriya Sun Yi Asarar Naira Tiriliyan 2.83

  • An samu asara mai yawa a kasuwar hannayen jari ta Najeriya, inda 'yan kasuwa suka rasa kimanin Naira tiriliyan 2.84
  • An ce Indeksin All-Share ya sauka da 2.99% zuwa maki 149,524.81, yayin da ribar shekara shekara ta ragu zuwa 45.3%
  • Rahoto ya nuna cewa barazanar Donald Trump na kawo hari Najeriya, fitar ribar masu jari ne suka jawo asarar da aka yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - A makon da ya gabata, kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX) ta fuskanci yanayi na raguwar darajar kayayyakin da ake kasuwancinsu.

An rahoto cewa darajar kasuwar ta sauka da Naira tiriliyan 2.84, daidai da kashi 2.90 cikin ɗari na raguwar jarin 'yan kasuwa a NGX.

'Yan kasuwa a NGX sun yi asarar Naira tiriliyan 2.84 bayan barazanar Trump
Kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX) da ke Legas. Hoto: @ngxgrp
Source: Getty Images

Alkaluman Indeksin All-Share ya kuma ragu da kashi 2.99 cikin mako guda zuwa 149,524.81, wanda ya sa ribar kasuwar ta shekara zuwa yau ta sauka zuwa 45.3%, daga 49.7%, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

An rage kudin Hajjin 2026 a Najeriya, NAHCON ta fitar da adadin da za a biya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tasirin baranar Trump a kasuwar hannun jari

Rahotanni sun nuna cewa barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da yuwuwar kai hari ga Najeriya, da kuma fitar ribar masu hannayen jari, sun taka rawa wajen sa kasuwar ta tsaya a jan layi tsawon mako ɗaya.

A ranar Litinin, masu jari sun fara fitar da hannayen jarin Aradel, AccessCorp da Dangote Sugar, wanda hakan ya ci gaba har zuwa Talata.

Zuwa ranar Laraba, masu jari sun karkata zuwa sayar da hannayen jarin Transcorp, MTN Nigeria da Lafarge, yayin da sashen bankuna ma ya fuskanci matsin lamba — musamman Ecobank, Access Bank da Zenith Bank.

Duk da cewa an samu ɗan motsi na saye a ƙarshen mako, kasuwar ta ci gaba da kasancewa cikin yanayin faduwar darajar wadannan kamfanoni, in ji rahoton The Cable.

Asarar da 'yan kasuwa suka tafka a NGX

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya kara yin kasa warwas a Najeriya', Minista ya bayyana dalili

Dukkan fannoni na kasuwa sun fuskanci a sara a wannan mako. Sashen Inshora ne ya fi yin asara da 7.6%, sakamakon sayar da hannayen jarin inshorar Sovereign Trust (-28.2%) da inshorar Cornerstone (-10.2%).

Bangaren Mai da Gas da Bankuna ma sun fuskanci asarar 4.8% da 3.9%, saboda faduwar farashin Oando (-16.8%), Aradel (-8.2%), AccessCorp (-10.0%) da ETI (-8.9%).

Sashen kayayyakin masarufi da kayayyakin masana’antu ma sun yi kasa da kashi 2.5% da 1.1%, saboda raguwar farashin Nestlé (-9.7%), Dangote Sugar (-8.1%), Lafarge (-6.4%) da Beta Glass (-10.0%).

An rahoto cewa kamfanonin NCR, Eunisell da wasu kadan ne kawai suka ci riba a kasuwar hannun jari ta Najeriya.
Hoton kwamfuta da ke nuna yadda ake hada-hada a kasuwar hannayen jari ta NGX. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Kamfanonin da suka ci riba da asara a NGX

A ɓangaren da suka ci riba akwai NCR (+20.9%), Eunisell (+20.2%), Union Dicon (+9.9%), Honeywell Flour (+9.5%), da UPDC (+6.8%), saboda an samu sababbin masu zuba jari.

Sai dai Sovereign Trust Insurance (-28.2%), C&I Leasing (-20.2%), SKY AVN (-19.0%), Berger (-17.4%), da International Energy Insurance (-17.0%) sun gamu da babbar asara, sakamakon ci gaba da matsin lamba daga masu sayarwa da raunin kwarin gwiwar masu saka jari.

Masana sun yi hasashen cewa kasuwar za ta ci gaba da kasancewa cikin yanayin na rashin tabbas a wannan mako, inda masu saka jari za su yi taka tsan-tsan.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ƴan bindiga sun farmaki dan majalisar Neja, an kashe jami'an tsaro

ICAN ta hango barazana ga Naira

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ƙungiyar masu akantoci ta kasa (ICAN), karkashin Chidi Ajaegbu, ta yi gargadin cewa darajar Naira na iya sake ruguzowa.

Chidi Ajaegbu ya yi hasashen cewa darajar kudin kasar nan zai fadi bayan zaɓen 2027, idan gwamnati ta ci gaba da karbo bashi ba tare da tsarin inganta kasa na.

Wannan na zuwa ne yayin da shugaban majalisar dokokin Enugu, Uche Ugwu, ya jaddada muhimmancin kasuwar hannayen jari wajen haɓaka kasuwanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com