'Ku Dawo Gida,' Shehu Sani Ya Aika Sako ga Wasu Ƴan Najeriya da Ke Zaune a Amurka
- Shehu Sani ya gargadi ‘yan Najeriya da ke zaune a Amurka da aka soke musu biza su gaggauta dawowa gida kafin a kama su
- Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta soke fiye da biza 80,000 tun watan Janairu 2025 saboda laifuffuka daban-daban
- Wannan na zuwa bayan Amurka ta ƙara tsaurara ƙa’idar neman bisa, ciki har da binciken shafukan soshiyal midiya na mutum
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya aika muhimmin sako ga 'yan Najeriya da ke da zama a kasar Amurka.
Shehu Sani ya shawarci ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka da suka samu matsalar biza a Amurka da su koma gida kafin hukumar ƙasar (ICE) ta kama su.

Source: Twitter
Sakon Shehu Sani ga mazauna Amurka
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Sani ya ce duk dadewar da mutum zai yi a ƙasar waje, akwai ranar da za a tuna masa cewa ba kasarsa ba ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon dan majalisar dattawan ya rubuta cewa:
“‘Yan Najeriya da dubban ‘yan Afirka da Shugaba Trump ya soke musu biza kwanan nan su hanzarta su bar ƙasar su koma gida kafin ICE ta kama su.
"Duk dadewar da za ka yi kana jin daɗin zama a ƙasar da yi ƙaura zuwa cikinta, rana ɗaya za a tuna maka cewa ba kasarka ta gado ba ce.”
Amurta ta soke biza 80,000 a ƙarƙashin Trump
Rahoton Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump ta soke akalla biza 80,000 tun daga watan Janairu 2025.
Wannan adadi ya ninka sau biyu na wanda aka soke a bara, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
An bayyana cewa daga cikin bizar da aka soke, 16,000 na da alaƙa da tukin mota cikin maye (DUI), 12,000 na da laifin kai hari, yayin da 8,000 suka shafi dalibai.
Rahoton ya kuma nuna cewa an soke wasu bizojin ne saboda zargi da tallafa wa ta’addanci, aikata laifi, barazana ga tsaro, da kuma wuce wa’adin zama.

Source: Getty Images
Amurka ta tsaurara ƙa’idar neman biza
A cikin sabon tsarin da Amurka ta fitar, duk masu neman bizar F, M, da J – wanda ake bayarwa ga dalibai da masu shirye-shirye – za su buɗe shafukan sada zumuntarsu domin karin bincike.
Wannan mataki na cikin ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da tsaro da tantance bayanan masu neman izinin shiga ƙasar.
Har ila yau, a watan Yuli 2025, Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da sauyin manufofi da ya rage wa’adin aiki na wasu nau’o’in biza da ‘yan Najeriya ke nema.
A cewar sanarwar, an dauki wannan mataki ne domin kare tsarin shige da ficen Amurka da tabbatar da cewa ƙasashen duniya, ciki har da Najeriya, sun bi ƙa’idojin tsaro da fasaha na duniya.
Amurka ta soke bizar Wole Soyinka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Wole Soyinka ya bayyana Donald Trump a matsayin “mai mulkin kama karya,” wanda ya yi kama da tsohon shugaban Uganda, Idi Amin.
Shahararren marubucin Najeriya kuma mai rike da lambar yabo ta Nobel, ya bayyana hakan ne lokacin da yake martani ga matakin Amurka na soke bizarsa.
Soyinka ya danganta janye masa biza da Amurka ta yi da tsauraran manufofin Donald Trump kan batun shige da fice, inda ya kafa sharadin sake karbar bizar kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


