Sarkin Musulmi da Wasu Manyan Mutane da Tinubu Ya Tattauna da Su kan Barazanar Amurka

Sarkin Musulmi da Wasu Manyan Mutane da Tinubu Ya Tattauna da Su kan Barazanar Amurka

Abuja, Najeriya - Barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ta kawo farmaki Najeriya ta ja hankalin manyan mutane a ciki da wajen kasar nan.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shugaba Trump ya yi barazanar ne bayan ya dauki matakin sanya Najeriya a cikin jerin kasashen da ake tauye 'yancin addini tare da zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Gwammatin Najeriya ta musanta wannan zargi da Shugaba Trump ya yi, tana mai cew matsalar tsaron kasar ta shafi kowa, kamar yada TVC News ta rahoto.

Duk da haka Trump ya kafe kan bakarsa, inda ya umarci ma'aikatar yaki ta Amurka ta fara shirin yiwuwar kai dauki Najeriya domin yakar yan ta'adda da kare rayukan kiristoci.

Tinubu ya maida martani ga Trump

Bayan haka ne Shugaba Bola Tinubu ya fito karara ya fada wa Shugaba Trump cewa Najeriya ba ta lamuntar wariya ko cin zarafin kowane addini a kasar.

Kara karanta wannan

Wasu takardu daga Amurka sun nuna wadanda suka 'zuga' Trump ya kawo hari Najeriya

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai mulkin dimokuradiyya wacce take bin kundin tsarin mulki da ke tabbatar da ’yancin addini ga kowa.

Sai dai duk da wannan martani da aka rika maida wa Trump, Shugaba Tinubu ya dauki matakin tattaunawa da wasu manyan mutane da shugabannin addinai.

Mutanen da Tinubu ya gana da su

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku wadanda Tinubu ya gana da su kan batun yancin addini da barazanar shugaban Amurka.

1. Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar

Daya daga cikin wadanda Bola Tinubu ya tattauna da su shi ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubaka III.

Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin Sarkin Musulmi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma'a da ta gabata, 7 ga watan Nuwamba, 2025.

Fadar shugaban kasa ta bayyana ganawar da Tinubu ya yi da Sarkin Musulmi a matsayin mai muhimmanci, inda ta ce wani bangare ne na tattaunawar da yake da shugabannin addinai.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

'Yadda mutuwar Gaddafi a Libya ke ci gaba da zama barazana ga Najeriya'

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sarkin Musulmi.
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III a Aso Rock Hoto: @DOlusegum
Source: Twitter

Sanarawar ta ce ganawar na daga cikin tattaunawan da shugaban ke yi da shugabannin addanai da sarakuna a Najeriya domin neman shawarwari kan zargin da Amurka ta yi.

Ta ce tattaunawar ta maida hankali ne wajen lalubo hanyoyin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Najeriya da tabbatar da ɗorewar ‘yancin addini a ƙasar nan.

"A ci gaba da tattaunawa da shawarwari da shugabannin addinai da na gargajiya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’adu Abubakar III," in ji Dada Olusegun.

2. Bishof Ignatius Ayau Kaigama

Jaridar The Cable ta rahoto cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da babban malamin addinin kirista, Archbishop Ignatius Kaigama na Abuja a fadar shugaban ƙasa a ranar Talata.

Ba a bayyana dalilin ganawar kai tsaye ba, amma ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa game da zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya da kuma barazanar Trump.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Najeriya ke tattaunawa da Amurka kan barazanar kawo hari

Shugaba Tinubu da Bishof Kaigama.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da Bishof Kaigama a Aso Rock da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Amma sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar bayan Bola Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi, ta ce duka tattaunawan ta maida hankali ne kan zaman lafiya da 'yancin addini.

Sanarwar ta ce wannan ganawa da Tinubu ya yi da Bishof Kaigama na cikin tattaunawar da yake yi da shugabannin addinai kan zargin kisan kiristoci da tauye yancin addini.

3. Shugaban ECOWAS, Julius Maada Bio

Shugaban kungiyar kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) kuma shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio ya ziyarci Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock da ke Abuja.

An ruwaito cewa Shugaba Maada Bio ya isa fadar shugaban Najeriya da misalin karfe 9:00 na daren ranar Juma'a, 7 ga watan Nuwamba, 2025.

ECOWAS na daya daga cikin kungiyoyin da suka fito suka musanta zargin tauye yancin addini ko kisan kiristoci da Amurka ta yi, ta na mai cewa babu inda hakan ke faruwa a Yammacin Afirka.

Kara karanta wannan

Tinubu: Fasto ya tura sako ga Trump kan kashe kashe da ake a Najeriya

Shugaban ECOWAS da Tinubu.
Hoton shugaban ECOWAS, Julius Maada Bio tare da Bola Ahmed Tinubu Hoto: @julius_maadabio
Source: Twitter

Wasu majiyoyi sun ce ganawar shugaban ECOWAS da Tinubu na da alaka da shirin Amurka na kawo farmaki domin yaki da yan ta'adda a Najeriya, wanda ya shafi batun tsaro.

A wata sanarwa da ya wallafa shafinsa na X, shugaban Saliyo ya ce ganawarsa da Tinubu tana da muhimmanci kuma sun tattauna abubuwan da suka shafi tsaro a Yammacin Afirka.

Shugaba Julius Maada Bio ya ce:

"Mun yi ganawa mai matukar muhimmanci da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
"A matsayina na shugaban ECOWAS, mun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro a Yammacin Nahiyar Afirka."

Najeriya ta fara tattaunawa da Amurka

A wani labarin, kun ji cewa Najeriya ta fara tattaunawa da Amurka kan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi ta kawo farmaki kasar.

Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris ya ce an fara tattaunawar diflomasiyya domin warware rudanin da ya shiga tsakanin Najeriya da Amurka kan batutuwan tsaro da hakkin ɗan adam.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Gwamnatin Tinubu ta fadi halin da ake ciki kan tattaunawa da Amurka

Haka kuma ya ce wannan tattaunawa na taimakawa wajen fayyace wasu kurakurai da rashin fahimta game da halin tsaron da Najeriya ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262