'Yan Ta'adda Sun Yi Kazamin Karo a Borno, An Kashe Mayakan ISWAP 50

'Yan Ta'adda Sun Yi Kazamin Karo a Borno, An Kashe Mayakan ISWAP 50

  • Fiye da ‘yan ta’adda 50 sun mutu a fada tsakanin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a Borno, musamman a yankin Abadam a wanu kazamin fada
  • ISWAP sun kai hari da jiragen ruwa 10 domin kwace wani tsibiri, amma JAS sun tsara dabarar tunkarar mayakan bayan an samu bayanan sirri
  • Wannan rikici ya nuna tsanantar rikici a tsakanin kungiyoyin ta’addanci biyu a yankin, lamarin da ya jefa fararen hula a cikin tashin hankali

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Rahotanni daga karamar hukumar Abadam na jihar Borno sun tabbatar da cewa fiye da ‘yan ta’adda 50 sun rasa rayukansu.

Wannan ya biyo bayan artabu a tsakanin tsagin Boko Haram na JAS da ISWAP a yankin Toumbun Gini, tsibiri a yankin Lake Chad, ranar Lahadi da yamma.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin Birtaniya, gwamnatin Tinubu ta fitar da sakamakon yaki da ta'addanci na 2025

'Yan ta'adda sun gwabza yaki a jihar Borno
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa mayakan ISWAP sun kai harin ne da jiragen ruwa 10 masu dauke da makamai masu karfi domin kwace tsibirin da JAS ta mamaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Borno: An yi artabu tsakanin 'yan ta'adda

Rahoton ya ce sai dai mayakan JAS sun samu labarin shirin ISWAP, lamarin da ya ba su damar shirya harin kwanton bauna a daidai lokacin da mayakan suka dura a tsibirin.

Wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

“A daidai 3.00 na rana, jiragen ruwan ISWAP sun sauka, amma abin da aka tsara a matsayin harin mamaye tsibiri ya juya zama tarko na kashe-kashe. Mayakan JAS sun rinjayi ISWAP cikin ‘yan mintuna, an kashe su.”

Rahotanni sun nuna cewa jiragen ruwa mayakan sun kwace jiragen ruwan ISWAP guda bakwai, yayin da wasu uku suka tsere amma sun jikkata sosai.

'Yan ta'adda na barazana ga fararen hula

Kara karanta wannan

Kogi: Jama'a sun barke da zanga zanga bayan 'yan bindiga sun jefa gawar tsohuwa a daji

Zagazola Makama, ya bayyana cewa wannan gumurzu da ya shiga kwana na biyar a tsakanin JAS da ISWAP a tafkin Chadi na jefa rayuwar mazauna yankuna.

Mayaka ISWAP fiye da 50 sun mutu
Taswirar jihar Borno, inda 'yan ta'adda suka gwabza yaki Hoto: Legit.ng
Source: Original

Makama ya yi gargadi cewa harin JAS na yanzu na iya tilasta wa mayakan ISWAP su tsere zuwa garuruwa kamar Kukawa, Monguno, da Marte, wanda zai kara barazana ga fararen hula da jami’an tsaro.

Ya kara da cewa wannan rikici ya raunana damar kungiyoyin biyu na kai manyan hare-hare, wanda zai bai wa jami'an taro damar karasa murkushe su duka.

Sojoji sun ceto mutane daga hannun 'yan ta'adda

A baya, kun samu labarin cewa rundunar sojin Najeriya ta gudanar da wani samame a yankin Buratai–Kamuya na jihar Borno bayan samun sahihan bayanai kan motsin ‘yan ta’adda.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi arangama a tsakanin sojoji da 'yan ta'addan da misalin ƙarfe 15.52 na rana, inda dakarun Najeriya suka rike wuta har ya tilastawa bata garin gudu wa.

Baya ga tarin mutanen da ake ceto, sojojin sun yi nasarar kwato makamai da suka hada da bindigar AK‑47 guda ɗaya, gidan harsasai biyar, motoci guda biyar, da babura guda biyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng