Abuja: Wike Ya Taso Masu Kadarori a Gaba, Ya Ba Su Kwanakin Biyan Tarar N5m

Abuja: Wike Ya Taso Masu Kadarori a Gaba, Ya Ba Su Kwanakin Biyan Tarar N5m

  • Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa masu gine-ginen da suka karya dokokin amfani da ƙasa wa'adin ceto kadarorinsu
  • Ministan ya shaida cewa har yanzu suna da damar gyara kuskuren da suka tafka idan suka biya rarar N5m a cikin kwanaki 14 masu zuwa
  • Wike ya ce waɗanda suka gaza biyan kudin a cikin wadannan kwanaki 14, za a ɗauki matakan tilasta masu bin dokar da aka tanada

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ministan babban birnin tarayya, Barista Nyesom Ezenwo Wike, ya sanar da cewa gwamnati ta bai wa masu kadarorin da suka karya dokokin amfani da ƙasa wa'adi.

Ya bayyana cewa mutanen da suka mallaki kadarori a wasu sassan Abuja na kwanaki 14 domin su biya tarar da aka ɗora masu.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin Birtaniya, gwamnatin Tinubu ta fitar da sakamakon yaki da ta'addanci na 2025

Wike ya bai wa masu kadarori a Abuja sabon wa'adin biyan tara
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa wannan sanarwar ta fito daga Lere Olayinka, mataimaki na musamman ga minista kan hulɗa da jama’a da kafofin sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya bai wa masu kadarori sabon wa'adi

The Sun Nigeria ta wallafa cewa a cikin sanarwar da Olayinka ya fitar a ranar Lahadi, ya ce kwanaki 30 da gwamnatin FCT ta bai wa masu gine-gine a watan Satumba ya zo karshe.

Ya bayyana cewa biyo bayan haka ne ya sa Wike ya amince da sabon wa’adin kwanaki 14, wanda zai fara daga Talata, 11 ga Nuwamba, 2025.

Wike ya bayyana cewa duk masu kadarorin da aka kama da laifin juya gidaje zuwa wuraren kasuwanci ba tare da izini ba, dole su biya tarar.

Wike ya ce dole a biya tarar N5m ko a fuskanci hukunci
Nyesom Wike, Ministan tarayyar Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

Wannan ya shafi masu kadarori a manyan tituna kamar Gana Street da Usuma Street a Maitama, Yakubu Gowon Crescent a Asokoro, da Aminu Kano Crescent a Wuse II.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

Sanarwar ta ce:

“Wanda bai biya cikin kwanaki 14 ba, gwamnatin babban birnin tarayya za ta ɗauki matakin aiwatar da doka kai tsaye."

Wike ya bai wa masu kadarori tabbaci

Olayinka ya kara da cewa duk masu kadarorin da suka biya tarar da kuma cika sharuddan gwamnati za su samu sababbin takardun mallaka na shekaru 99.

Ya bayyana cewa wannan shiri bai shafi kadarorin da aka riga aka soke mallakarsu saboda rashin biyan harajin ƙasa, ko kuma gaza wa wajen gina kadarorin a lokacin da aka tsara ba.

Wasu daga cikin masu kadarorin da suka shiga cikin jerin wadanda abin ya shafa sun hada da tsohon shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje.

Sai kadarar tsohon gwamnan Osun, Olagunsoye Oyinlola, tsofaffin alkalai na kotun koli Atanda Fatai-Williams da Aloma Mariam Mukhtar, da kuma kamfanin NNPC Limited.

Sowore ya rubuta takarda kan kadarorin Wike

A baya, kun ji mai rajin haƙƙin ɗan adam, Omoyele Sowore, ya gabatar da ƙorafi ga Lauyan Jihar Florida, James Uthmeier, inda ya zargi Nyesom Wike da sayen gidaje da kudin haram.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Uba Sani ya aika sakon gargadi ga 'yan siyasa

Sowore ya yi zargin cewa Wike, wanda a yanzu minista ne a Najeriya ya sayi gidaje uku a Winter Springs, Florida tsakanin 2021 zuwa 2023, da kuɗi da ake zargin na sata ne.

Lauyan Sowore, Deji Adeyanju, ya shigar da ƙorafin a ranar 22 Satumba 2025, ya kuma bayyana cewa an haɗa hujjoji da dokokin Florida da na Tarayyar Amurka a kan batun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng