'Yan Bindiga Sun Shiga Kano da Makamai, Sun Sace Mata
- ‘Yan bindiga sun farmaki kauyen Yan Kwada da ke yankin Faruruwa a karamar hukumar Shanono da ke jihar Kano
- An bayyana halin da ake ciki bayan 'yan ta'addan sun samu nasarar sace mata biyar ciki har da masu shayarwa
- Rahotanni sun nuna cewa har yanzu gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sandan Kano ba su ce komai ba game da lamarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - ‘Yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Yan Kwada da ke yankin Faruruwa a karamar hukumar Shanono, jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne a daren Lahadi, inda suka sace mata biyar ciki har da masu shayarwa.

Source: Original
Rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa wasu daga cikin matan sun kubuta daga hannun 'yan bindigar.

Kara karanta wannan
Kogi: Jama'a sun barke da zanga zanga bayan 'yan bindiga sun jefa gawar tsohuwa a daji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kai hari Kano aka sace mata
Shaidun gani da ido sun ce maharan sun iso kauyen cikin tarin yawa, dauke da muggan makamai, suna harbe-harbe kafin su shiga gidaje domin yin garkuwa da mutanen da suka so.
Wani mazaunin kauyen ya shaida cewa ‘yan bindigar sun shigo cikin dare, suna harbi da tsoratar da jama'a kafin su yi awon gaba da mata biyar.
Ya kara da cewa bayan harin, daga cikin matan da aka sace, biyu sun dawo gida, yayin da uku suka rage a hannun masu garkuwan.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan harin ya faru ne mako guda bayan da dakarun soji suka fafata da ‘yan bindiga a yankin, inda aka kashe 'yan ta'adda 19 daga cikin su.
Fargaba ta mamaye wasu mazauna Kano
Al’ummar yankin Faruruwa da makwabtansu da ke tsakanin jihar Kano da Katsina sun shiga cikin halin fargaba sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.
Wasu daga cikin mazauna kauyukan sun bar gidajensu saboda tsoron sake faruwar irin wannan hari, yayin da wasu suka nemi mafaka a cikin garin Faruruwa.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa:
“Kowane dare yanzu muna cikin fargaba. Ba mu san lokacin da za su sake shigowa ba, saboda haka mutane da dama sun bar kauyukan zuwa cikin birane.”
Hukumomi a Kano ba su ce komai ba
Duk da tsananin fargabar da ke tattare da mazauna yankin, gwamnatin jihar Kano da rundunar ‘yan sanda har yanzu ba su fitar da wata sanarwa ba game da harin.

Source: Facebook
A lokacin hada wannan rahoton, Legit Hausa ta bibiyi shafin Facebook na mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa amma bai fitar da sanarwa ba.
Haka zalika, kakakin 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa bai wallafa wani sako game da lamarin ba a shafinsa na Facebook.
An yi zanga zanga a jihar Kano
A wani labarin, kun ji cewa wasu magoya bayan kungiyar IMN karkashin Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi zanga zanga a Kano.
Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zanga zangar ne domin adawa da matakin shugaban Amurka na kawo farmaki kasar nan.
Donald Trump ya yi barazanar kawo hari Najeriya ne yayin da ya yi zargin cewa ana kashe Kiristoci masu yawa a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

