Dakarun Sojoji Sun Yi Arangama da 'Yan Ta'adda a Borno, An Kubutar da Mutane 86
- Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 86 da aka yi garkuwa da su a tsakanin yankin Buratai–Kamuya, jihar Borno
- Dakarun sun kuma lalata sansanin 'yan Boko Haram/ISWAP, yayin da aka kwato makamai, motoci, da kayan abinci
- Bugu da kari, sojojin sun samu nasarar kama mutane 29 da ake zargin suna kai kayayyaki ga ‘yan ta’adda a yankin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutane 86 da aka yi garkuwa a yankin Buratai–Kamuya na jihar Borno.
Dakarun sojojin, sun kuma kaddamar da hare-hare kan sansanin Boko Haram/ISWAP da ke yankin, kuma sun lalata shi gaba daya.

Source: Twitter
Sojoji sun yi arangama da 'yan ta'adda
Zagazola Makama, mai sharhi kan lamuran tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas da kuma Tafkin Chadi ne ya fitar da rahoton a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoto daga rundunar musamman ta 135 da ke Buratai, ya nuna cewa an gudanar da wannan samamen ne a ranar Lahadi bayan an samu sahihan bayanai kan motsin ‘yan ta’adda a hanyar Buratai–Kamuya.
Majiyoyi sun ce da misalin ƙarfe 3:52 na yamma, sojojin da ke Echo 1 (Dutse Kura) sun yi arangama da ‘yan ta’adda, wadanda suka bude masu wuta.
Jin abin da ya faru ya sa aka tura ƙarin sojoji cikin gaggawa, inda suka hadu suka fatattaki maharan kuma suka bi sahunsu har cikin dajin Mangari.
An kubutar da mutane 86 daga 'yan bindiga
A yayin wannan hari, ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin tserewa da mutanen da suka sace a cikin motoci guda biyu.
Sai dai, an rahoto cewa sojojin sun yi musu kwanton-bauna, suka yi masu ruwan harsasai da ya tilasta su tserewa suka bar motocin.
Bayan sun tsere, sojoji sun kuma bi sahunsu, har suka gano sansanin Boko Haram/ISWAP, inda a cikinsa aka gano tare da kubutar da mutane 86 — maza, mata da yara.
An kuma kwato makamai da kayayyaki masu yawa ciki har da bindigar AK-47 guda ɗaya, gidan harsasai biyar da ke cike da harsasai 73, madaurin wando na PKT guda hudu, motoci biyar, babura biyar, kekuna guda takwas da Keke Napep guda biyu.
Bayan an kubutar da mutanen, an kuma alkinta kayayyakin da aka kwato, sai sojoji suka tarwatsa sansanin nan take.
Sojoji sun kama masu taimaka wa Boko Haram
A wani samame na daban, sojojin da ke a sansanin Delta 1 a Mangada sun kama mutane 29 da ake zargin suna kai wa 'yan ta'addar Boko Haram kayayyaki.
An tabbatar da cewa mutum takwas daga cikinsu suna aiki kai tsaye da ‘yan ta’addan wajen kawo man fetur, magunguna da bayanan sirri.
An kwato motoci biyu cike da fetur, keke Napep ɗaya, jarkuna 38, tayoyi, magungunan jinyar raunukan harbi da kuma kayan abinci masu yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa za a mika dukkan waɗanda aka kama da kayan ga rundunar hadin gwiwa ta 27 domin ci gaba da bincike.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

