'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Yi Ta'asa a Kebbi, Sun Hallaka Jami'in Hukumar Kwastam
- Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton na kungiyar Lakurawa ne sun kai harin ta'addanci a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma a Najeriya
- 'Yan ta'addan na Lakurawa sun hallaka wani jami'in hukumar Kwastam da ke aiki a karamar hukumar Bagudu ta jihar Kebbi
- Lamarin ya sanya fargaba a zukatan jami'an hukumar kwastam musamman wadanda ke gudanar da ayyukansu a bakin iyaka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Lakurawa ne sun kashe wani jami'in hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) a jihar Kebbi mai suna DSC S. Muhammad.
'Yan ta'addan na Lakurawa sun kashe jami'in na Kwastam ne a sansaninsu da ke kan iyaka a Maje, karamar hukumar Bagudu a jihar Kebbi.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin tsakiyar daren ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan
Kebbi: Mataimakin shugaban majalisa ya kubuta daga hannun 'yan bindiga, an ji yadda ya tsira
'Yan Lakurawa sun kashe jami'in Kwastam
Lamarin ya auku ne lokacin da maharan suka kai farmaki sansanin kwastam na Maje, inda suka bude wuta kan jami'an da ke wurin.
Jaridar The Punch ta ce a yayin harin sun harbe jami'in hukumar tare da bankawa sansanin wuta.
An kai gawar marigayi Muhammad zuwa asibitin koyarwa na tarayya (FTH), Birnin Kebbi, yayin da ake shirin binne shi a ranar Lahadi.
Jami'an kwastam sun shiga firgici
Harin ya jefa jami’an kwastam da ke aiki a yankunan bakin iyaka cikin firgici da tsoro, inda da dama daga cikinsu ke nuna damuwa kan tsaron rayukansu.
Barazanar da ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa ke yi ta jawo tsoro da rashin kwanciyar hankali a yankin, lamarin da ke hana jami’an aiwatar da aikinsu yadda ya kamata.
Wannan sabon harin na zuwa ne a jerin hare-hare da aka kai a kwanakin baya kan jami’an tsaro da fararen hula a jihar Kebbi, abin da ke nuna bukatar ƙarfafa tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan
Hukumar INEC ta dora sama da 75% na sakamakon zaben gwamnan Anambra a shafin IReV

Source: Original
Karanta wasu labaran kan hukumar kwastam
- Katsina: An tsinci gawar jami'in Kwastam bayan kwana da mata 3 a otal
- Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba
- FIRS, Kwastam da hukumomi 3 sun tatso Naira tiriliyan 21 daga hannun ƴan Najeriya
- Kwastam ta cafke mota makare da sinadaran hada bam da wasu haramtattun kaya
- 'Yan ta'addan Lakurawa sun kai farmaki a Kebbi, sun hallaka jami'an tsaro
'Yan ta'adda sun kashe mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindigan da ke da biyayya ga hatsabibin dan ta'adda sun kai hari a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun kashe mutum biyar tare da sace wasu tara a kauyen Bargaja, yayin harin da ya tayar da hankulan mutane a yankin
Hakazalika, rahotanni sun bayyana cewa mafi yawancin mutanen da 'yan bindigan suka sace yayin harin yan mata ne masu kananan shekaru.
Asali: Legit.ng