‘Abin da Rasha, China Za Su Yi bayan Harin Amurka’: Malami Ya Gargadi Tinubu
- Fitaccen Fasto a Najeriya, Enoch Adeboye ya roƙi Shugaba Bola Tinubu na kasar da ya nemi sulhu ta diflomasiyya da Amurka
- Malamin ya bayyana haka ne bayan barazanar harin soja da Donald Trump ya yi ga Najeriya kan zargin kisan Kiristoci
- Ya gargadi gwamnatin Tarayya cewa idan Amurka ta kai hari, babu wata ƙasa da za ta taimaka wa Najeriya face yin suka kawai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Babban Faston Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu.
Faston ya bukaci Tinubu da ya bi hanyar diflomasiyya kan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi na daukar mataki kan Najeriya.

Source: Twitter
Gargadin Fasto ga Tinubu kan barazanar Trump
Adeboye ya ce ya zama dole Najeriya ta yi magana da Amurka cikin gaggawa, domin idan har aka kai hari, babu wanda zai taimaka, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Ina tabbatar muku, idan Amurka ta kai hari, babu ƙasar da za ta kare mu. Su dai za su yi suka ne kawai.”
Ya ƙara da cewa waɗanda ke kewaye da shugaba Tinubu ba sa ba shi shawara mai kyau game da yadda ake magance matsalar tsaro a ƙasar.
Adeboye ya bayyana haka ne bayan maganganu da ake ta yi game da barazanar da Donald Trump ya yi ga Najeriya.
Ya kara da cewa:
“Idan na ji jawabin shugaban kasa, musamman kan tsaro, inda aka ce komai ya daidaita, sai na yi mamaki sosai.”

Source: Getty Images
Shawarar da Fasto Adeboye ya ba Tinubu
Faston ya shawarci gwamnati ta ba shugabannin tsaro wa’adin kwanaki 90 domin su kawar da ‘yan ta’adda ko kuma a sauke su daga mukamansu.
Ya ce ya taba ba da irin wannan shawara ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma ba a ci gaba da aiwatar da ita yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan
Fasto Adeboye ya kawo mafita, ya aika sako ga Shugaba Tinubu kan barazanar Amurka
Adeboye ya roƙi Tinubu da ya nemi Shugaban Amurka ta hanyar diflomasiyya, domin samun jinkiri na kusan kwana 100 kafin a ɗauki matakin soja.
TheCable ta ce Faston ya ce ya kamata gwamnati ta tursasa jami’an tsaro su kama masu ɗaukar nauyin ta’addanci, ko da kuwa manyan mutane ne a ƙasar.
“Ina roƙon gwamnati ta yi gaggawa wajen kawo ƙarshen kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa, domin rayukan mutane ba na wasa ba ne.”
- Enoch Adeboye
Adeboye ya jaddada cewa wannan lamari ba na addini ba ne, yana shafar Musulmai da Kiristoci gaba ɗaya, saboda haka gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa.
Barazanar Trump: Fasto ya ba Tinubu shawara
Kun ji cewa Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa tun da aka fara kashe kiristoci a Najeriya, ya ankarar da shugabannin kasar don daukar mataki.
Babban limamin cocin RCCG ya shawarci Shugaba Tinubu ya dauki matakan gaggawa tun kafin Amurka ta fara kawo hari.
A cewarsa, ya kamata Tinubu ya ba hafsoshin tsaro wa'adin watanni uku su kawar da yan ta'adda ko kuma su yi murabus.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
