An Kai Karar Gwamna Dauda Wurin Trump, an Bukaci Ya Kakaba Masa Takunkumi

An Kai Karar Gwamna Dauda Wurin Trump, an Bukaci Ya Kakaba Masa Takunkumi

  • Wata ƙungiya mai suna 'Concerned Nigerians for Human Security' ta rubuta wa Donald Trump wasiƙa kan Gwamna Dauda Lawal
  • Kungiyar ta bukaci Trump ya shiga tsakani kan tsananin rashin tsaro a Zamfara da Arewacin Najeriya wanda ya jawo asarar rayuka
  • Ta kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta ayyana dokar ta-baci a Zamfara, don dakatar da kisan jama’a da ake yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Wata ƙungiya mai suna 'Concerned Nigerians for Human Security' ta taso Gwamna Dauda Lawal Dare a gaba kan rashin tsaro a Zamfara.

Kungiyar ta roƙi shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, da ya ɗauki mataki kan matsalar tsaro da ta ƙara ta’azzara a jihar da wasu sassan Arewacin Najeriya.

An bukaci Trump ya tsoma baki kan matsalar tsaro a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal Dare da Donald Trump. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Zamfara: Kungiya roki Trump ya dauki mataki

Ƙungiyar ta bayyana haka a cikin wata budaddiyar wasiƙar da ta aika masa wanda wakilin Legit.ng ya samu a jiya Asabar 8 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Amurka ya kuma jan kunnen Tinubu kan wasa da barazanar Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubuta wasikar musamman saboda cewa kashe-kashe da sace-sacen jama’a a Zamfara sun zama babbar masifa.

Ta ce dubban jama’a ciki har da mata da yara sun mutu ko an sace su daga lokacin da ‘yan ta’adda suka mamaye ƙauyuka.

Ƙungiyar ta zargi gwamnati da gazawa da rashin gaskiya wajen kula da kuɗaɗen tsaro da aka ware don kare rayuka, tana mai cewa hakan ne ya janyo rashin shugabanci da karancin amincewa daga jama’a.

A cikin wasiƙar, ƙungiyar ta roƙi gwamnatin Amurka ta saka takunkumin biza ga wasu manyan ‘yan siyasa, musamman Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, tana mai cewa hakan zai matsa musu lamba su daina yin amfani da jinin jama’a don ribar siyasa.

An kai karar gwamna Dauda Lawal wurin Trump kan matsalar tsaro
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da ke fama da rashin tsaro. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Bukatar kungiyar ga Trump, gwamnatin tarayya

Ƙungiyar ta bayyana cewa “Shugabanci amana ce, ba gata ba,” tana mai cewa wannan mataki zai hana shugabanni jin daɗin yawon ƙasashen waje.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci a Zamfara, tana mai cewa rikicin ba na addini ba ne, domin Musulmi da Kiristoci duka suna fuskantar irin wannan tashin hankali.

Kara karanta wannan

Reshe zai juye da mujiya, Gwamna mai ci ya zargi 'yan adawa da sake kudi a zabe

“Wadannan kashe-kashen ba na addini ba ne, hakan ya faru sakamakon gazawar gwamnati ne, cin hanci, da rashin kula da kuɗin tsaro.”

Ta yabawa matakan da Shugaba Bola Tinubu ke ɗauka na ƙara ƙarfafa tsaro da tura jami’ai na musamman, amma ta ce hakan ba zai yi tasiri ba idan gwamnatocin jihohi ba su nuna gaskiya da jajircewa ba.

Ƙarshe, ƙungiyar ta roƙi tallafin ƙasashen waje da taimakon ɗabi’a don kawo ƙarshen kisan jama’a da kauracewa gidaje da ke ta faruwa a Zamfara da Arewacin ƙasar.

An roki Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Zamfara

A baya, mun ba ku labarin cewa wata ƙungiyar Arewa ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara saboda tabarbarewar tsaro.

Kungiyar NCAJ ta zargi gwamnatin Zamfara da yin salon mulkin 'kama karya' yayin da ta ce jihar ba ta samun wani ci gaba a yanzu.

NCAJ ta ce garuruwa sun koma biyan haraji ga ‘yan bindiga, jami’an gwamnatin jihar na amfana da haramtacciyar hakar ma’adinai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.