Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Mata 9 a Sokoto, Sun Hallaka Wasu
- Akalla mutum biyar sun mutu yayin da aka sace mata tara a harin da ’yan bindiga suka kai wani kauye a jihar Sokoto
- 'Yan bindigar da ake zargin yaran Bello Turji ne, sun kai farmakin ne da daddare, inda suka kona gidaje da kashe bayin Allah
- Gwamnatin karamar hukumar ta Isa ta karyata zargin cewa shugabanta ya yi sakaci da rahoton leken asiri kafin harin ya faru
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - A kalla mutum biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da aka sace wasu mata tara bayan harin da ’yan bindiga suka kai kauyen Bargaje, karamar hukumar Isa a jihar Sokoto, a daren Juma’a.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar, waɗanda ake zargin yaran Bello Turji ne, sun mamaye kauyen haye a kan babura, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi tare da kona gidaje.

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Wasu mazauna yankin sun ce 'yan bindigar sun shafe tsawon sa’o’i suna cin karensu ba babbaka, inda jama’a da dama suka gudu cikin dazuzzuka domin tsira da rayukansu, in ji Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin kauyen ya shaida cewa ’yan bindigar sun shigo daga gabashin kauyen da misalin ƙarfe 11:00 na dare, inda suka kashe mutum biyar sannan suka yi awon gaba da mata tara.
Mutumin ya ce:
“Sun farmake mu ne kwatsam, babu wanda ya yi zato. Matasan da ke dan yin aikin sa kai sun yi ƙoƙarin ba da kariya amma 'yan bindigar sun fi ƙarfin su."
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ’yan sanda ba su fitar da sanarwa a hukumance ba, ko da yake wani jami’in tsaro ya tabbatar da harin amma ya ƙi bayyana adadin mutanen da suka mutu.
Gwamnati ta karyata zargin sakacin ciyaman
A wata sanarwa da majalisar karamar hukumar Isa ta fitar a ranar Asabar, ta bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta suna cewa shugaban karamar hukumar, Sharehu Kamarawa, ya yi sakaci da bayanan leken asiri kafin harin — ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan
Abu ya tsananta: Mutane sun tsere daga gidajensu kan hare haren 'yan bindiga a Kano
“Mun ɗauki mataki cikin gaggawa bayan samun rahoton hatsarin, mun tura jami’an tsaro da matasa 'yan sa-kai domin hana farmakin, amma ’yan bindigar suka canza hanya kuma suka kai hari ta Bargaje,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ce an dakatar da kwamandan tsaro na yankin tare da sauya shi da sabon kwamanda domin inganta tsarin tsaro.

Source: Twitter
An gargadi mutane kan yada karya
Shugaban karamar hukumar, Sharehu Kamarawa, ya jaddada cewa gwamnatin sa na ci gaba da tallafawa jami’an tsaro da kayan aiki, man fetur, da kara sama masu walwala.
Ya kuma gargadi jama’a da su guji yada labaran ƙarya, yana mai cewa hakan na iya ruguza ƙoƙarin tsaro da kuma ƙarfafa wa ’yan ta’adda gwiwa.
“Tsaro alhakin kowa ne. Muna buƙatar haɗin kai, tsaro, da sahihan bayanai — ba wai jita-jita ba."
- Sharehu Kamarawa.
'Yan bindiga sun fafata da mafarauta a Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa, aƙalla mafarauta 11 na sun rasa rayukansu sakamakon musayar wuta mai tsanani da ƴan bindiga a jihar Sokoto.
Arangamar ta faru ne a ranar Juma’a, lokacin da mafarautan suka hana wasu ƴan bindiga kusan 40 kai hari a ƙauyen Magonho, kamar yadda ganau suka shaida.
Wani mazaunin yankin ya ce ƴan bindigar suna ɗauke da manyan makamai, kuma sun fara buɗe wuta bayan da aka hana su kai harin da suka shirya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

