Anambra: An Fadi Yawan Ƙananan Hukumomi da Soludo ya Lashe, Ya Nakasa APC

Anambra: An Fadi Yawan Ƙananan Hukumomi da Soludo ya Lashe, Ya Nakasa APC

  • An fara shirin sanar da sakamakon zaben jihar Anambra da aka gudanar a jiya Asabar 8 ga watan Nuwambar 2025
  • Gwamna Charles Soludo na jam’iyyar APGA yana kan gaba a zaben gwamnan da ratar kuri'u masu yawa wanda ke nuna shi ne da nasara
  • Hukumar INEC ta tabbatar da cewa jam'iyyar APGA mai mulki ce ke kan gaba bayan lashe kananan hukumomi 19

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - An tabbatar da cewa dan takarar jam’iyyar APGA, Gwamna Charles Chukwuma Soludo, yana kan gaba a zaben jihar Anambra.

An Soludo ya lashe mafi yawan kananan hukumomi a zaben gwamna da aka gudanar a Jihar Anambra ranar Asabar 8 ga watan Nuwambar 2025.

Ana dakon sakamakon zabe a Anambra
Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra. Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo.
Source: Facebook

Ana ci gaba ta tattara sakamakon zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara tara sakamako a ofishinta da ke birnin Awka a jihar, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Soludo ya lallasa APC, LP, ya ci zabe a dukkan kananan hukumomi 21

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan kammala kirga kuri’u a yawancin rumfunan zabe da ke fadin jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Tun farko, hukumar zabe ta ce babu wata matsala a zaben yayin da mutane suka fito kwansu da kwarkwata domin tabbatar da cewa sun zabi dan takarar da suke muradi.

Yawan ƙananan hukumomi da Soludo ya lashe

Daga cikin kananan hukumomi 19 da aka bayyana, APGA ta samu kuri’u 389,789, yayin da jam'iyyar APC ta samu 91,592, Sai LP ta samu 10,366, sai PDP da 1,230 kacal.

Anambra tana da kananan hukumomi 21, kuma yanzu saura biyu da ba a bayyana sakamakonsu ba, abin da ke ba Soludo babban damar sake lashe zabe.

INEC ta bayyana cewa jimillar masu kada kuri’a da aka yi wa rajista su ne 2,802,790, ciki har da 140,370 sabbin masu kada kuri’a daga mazabu 326.

Soludo ya lashe zabe a dukan ƙananan hukumomin Anambra
Taswirar jihar Anambra da aka gudanar da zaben gwamna. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda Gwamna Soludo ke kan gaba a zaben

Kara karanta wannan

Aiki ya zo karshe, INEC ta dora kaso 99% na sakamakon zaben gwamnan Anambra a IReV

Zaben ya gudana a rumfunan zabe 5,718, yayin da biyu ba su da masu rajista, jam’iyyu 16 ne suka tsayar da ‘yan takara, ciki har da mata biyu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sakamakon da aka bayyana ya nuna Soludo ya fi rinjaye a yawancin yankuna, ciki har da Awka South, Aguata, da Njikoka, inda APGA ta samu kuri’u masu yawa sosai.

Yanzu idanu na kan sauran kananan hukumomi biyu, domin tabbatar da cewa Soludo zai iya tabbatar da nasarar neman wa’adinsa na biyu a jihar Anambra.

Sayan kuri'a: Gwamna Soludo ya zargi yan adawa

A baya, an ji cewa Gwamna Charles Soludo ya yi magana yayin da ake gudanar da zaben jihar Anambra a ranar Asabar 8 ga wata Nuwambar 2026.

Soludo ya zargi wata jam’iyyar adawa da sayen ƙuri’u da makudan kudi, yayin da yake nuna kwarin gwiwa kan nasarar APGA.

Farfesa Soludo ya ce an samu ƙalubale da na’urar BVAS a wasu wurare kamar Olumbanasa da Nnewi ta Kudu a Anambra.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.