Dan Majalisar Amurka Ya Kuma Jan Kunnen Tinubu kan Wasa da Barazanar Trump

Dan Majalisar Amurka Ya Kuma Jan Kunnen Tinubu kan Wasa da Barazanar Trump

  • Dan majalisar Amurka, Riley Moore, ya kuma gargadin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kan barazanar Donald Trump
  • Moore ya gargadi gwamnatin Najeriya da ka da ta raina nufin Shugaba Donald Trump wajen dakatar da kisan Kiristoci
  • Ya ce Trump zai ɗauki matakai masu tsauri idan tashin hankalin ya ci gaba, yana mai kira ga Najeriya ta haɗa kai da Amurka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Dan majalisar Amurka, Riley Moore, ya gargadi gwamnatin tarayyar Najeriya game da barazanar Donald Trump.

Moore ya gargade ta da ka da ta raina nufin Shugaba Donald Trump wajen ɗaukar mataki kan kisan Kiristoci da ke ci gaba a ƙasar.

Dan majalisar Amurka ya tura sakon gargadi ga Tinubu
Shugaba Donald Trump da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Hakan na cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar 8 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya jawo barazanar Trump ga Najeriya

A kwanan nan, Trump ya ce Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana ta gaske daga masu tsattsauran ra’ayi na Musulunci.

Ya bayyana cewa “dubban Kiristoci suna rasa ransu" yana mai zargin ‘yan ta’adda da aikata wannan ta’asa, sannan ya sanya Najeriya cikin jerin kasashe masu matsala ta addini.

Trump ya kuma ce Amurka “ba za ta tsaya ba tana kallo ana aikata irin waɗannan ta’addanci ba,” yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta kare Kiristoci a duniya.

Umarnin Trump ga yan majalisar Amurka

Haka kuma ya umurci ‘yan majalisa su binciki lamarin, inda ya bai wa Riley Moore, Tom Cole, da Kwamitin Kudin Majalisa umarni su ba shi rahoto.

Trump ya bayyana cewa ya umarci Pentagon ta fitar da matakan soja a Najeriya domin kare al’umman Kiristoci daga ‘yan ta’adda.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta karyata zargin, inda Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa ƙasar tana mutunta ‘yancin addini da kare ‘yan ƙasa ba tare da wariya ba.

Kara karanta wannan

'Abin da zan faɗawa Trump ido da ido, idan na haɗu da shi': Barau Jibrin ya fusata

A halin yanzu, barazanar matakin soja daga Amurka ta jawo hankalin ƙasashen duniya, ciki har da Rasha da China, waɗanda suka nuna goyon baya ga Tinubu.

Dan Amurka ya sake jan kunnen Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana jawabi a taro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Gargadin Riley Moore ga gwamnatin Najeriya

Moore ya bayyana cewa Shugaba Trump yana da cikakken niyyar ɗaukar matakan da suka dace idan rikicin bai tsaya ba.

Ya ce:

“Ka da ku kure hakurin shugaba Trump, yana da niyya kuma da gaske yake ya kawo ƙarshen kisan gilla da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.”

Moore ya kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta yi abin da ya dace ta hanyar haɗa kai da Amurka wajen kare rayukan Kiristoci da kawo ƙarshen wannan rikici.

An ƙaryata shigowar sojojin Amurka Najeriya

Mun ba ku labarin cewa Fadar shugaban kasa ta yi magana bayan yada wani bidiyo a kafofin sadarwa da aka ce sojojin Amurka sun fara sauka a Najeriya.

An yada wani faifan bidiyo da ya bazu a intanet da ke cewa sojojin Amurka sun isa Jihar Rivers domin kaddamar da umarnin Donald Trump.

Mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, ya bayyana cewa labarin karya ne kawai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.