Abin a Yaba: EFCC Ta Kwato N42.5m da Ma'aikaciyar Banki Ta Sace wa Ƴar Shekara 70

Abin a Yaba: EFCC Ta Kwato N42.5m da Ma'aikaciyar Banki Ta Sace wa Ƴar Shekara 70

  • EFCC ta mayar wa wata tsohuwa mai shekara 70, Margret Taye Odofin, N42.5m da jami’ar banki ta sace mata
  • Hajiya Odofin ta ce ta yi jira na shekaru kafin ta samu adalci, tare da yabawa EFCC da shugabanta bisa jajircewarsu
  • Hukumar ta ce za ta ci gaba da tumurmusar masu aikata laifin kudi har sai an dawo wa wadanda aka zalunta hakkokinsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar EFCC ta mayar wa wata dattijuwa kuma ma’aikaciyar gwamnati mai ritaya, Margret Taye Odofin, kudi har N42.5m da wata jami’ar banki ta kwashe mata.

An mika kudin da aka kwato daga hannun wacce ake zargi, Misis Kehinde Olawale Yusuf, ga Odofin a ofishin EFCC na Kaduna.

EFCC ta samu nasarar mayar da N42.5m ga dattijuwa 'yar shekara 70 da aka kwato kudinta da aka sace.
Mukaddashin daraktan EFCC na Kaduna, Bawa Kaltingo ya na mika takardar kudi N42.m ga dattijuwa. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

Mukaddashin daraktan hukumar na Kaduna, Bawa Kaltungo, ya gabatar da kudin ga Margret a madadin Mista Ola Olukoyede, kamar yadda aka wallafa a shafin EFCC na X.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

Yadda jami'ar bankin ta kwashe kudin tsohuwa

Rahotanni sun bayyana cewa, Odofin ta shigar da korafi ga EFCC a watan Disamba 2024 bayan ta gano cewa jami’ar bankinta ta karkatar da kudin ajiyarta zuwa wasu asusu daban-daban ba tare da izini ba.

Ta bayyana cewa Kehinde Yusuf ta yaudare ta da wani tsarin jarin bogi a shekarar 2020, inda ta ba ta tabbacin cewa za ta rika samun riba ta N1.7m a duk bayan watanni uku.

Amma daga baya Odofin ta gano cewa jami'ar bankin ta wawure mata N47m daga asusunta zuwa wasu asusun baki daban daban.

Binciken EFCC ya gano cewa Kehinde Yusuf ta tsere zuwa kasar Burtaniya bayan badakalar ta tonu, sai dai hukumar ta bi sahunta har ta sami nasarar kwato wasu daga cikin kudin da aka sace.

Dattijuwa ta fashe da kuka a ofishin EFCC

Da ake mika kudin, Odofin ta fashe da kuka na farin ciki, tana yabawa hukumar EFCC da shugabanta bisa jajircewarsu wajen dawo mata da hakkinta bayan shekaru da dama tana jira.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ƴan bindiga sun farmaki dan majalisar Neja, an kashe jami'an tsaro

Ta ce:

“Ban taba tunanin hakan zai faru ba. Mun kai rahoto a Birtaniya, amma aka ce laifin an aikata shi ne a Najeriya, don haka EFCC ce kadai za ta iya taimaka mun.
"Yau Allah ya yi amfani da hukumar wajen share min hawaye na. Zan ci gaba da yaba wa EFCC saboda sun tabbatar min cewa har yanzu akwai adalci a Najeriya.”
Hukumar EFCC ta ce za ta kara kaimi wajen yaki da masu aikata laifuffukan kudi.
Jami'an hukumar EFCC sun fito bakin aiki. Hoto: @officialEFCC
Source: UGC

EFCC ta ce babu sassauci ga masu aikata laifi

Da yake jawabi yayin mika kudin, Kaltungo ya ce wannan nasara alama ce ta yadda hukumar ke tabbatar da adalci da kare hakkin wadanda aka zalunta.

Ya ce:

“Muna godiya gare ku saboda amincewar da kuka yi da mu. Wannan nasarar shaida ce cewa EFCC tana aiki cikin gaskiya da kwarewa.”

Ya kara da cewa, a karkashin jagorancin Olukoyede, hukumar ta kuduri aniyar fatattakar masu aikata laifuffukan kudi tare da tabbatar da cewa wadanda aka zalunta sun samu adalci.

Kara karanta wannan

Rikici tsakanin lauya da Sheikh Gumi ya canja salo, ana shirin dangana wa ga kotu

EFCC ta gayyaci shugaban NAHCON

A wani labarin, mun ruwaito cewa, EFCC na binciken shugaban NAHCON, Farfesa Saleh Abdullahi Usman, bisa zargin karkatar da kudi a Hajjin 2025.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin an karkatar da sama da Naira biliyan 50 wajen kwangiloli da tafiye-tafiye ba bisa ka’ida ba.

Hakan na zuwa ne bayan gayyatar wasu jami'an hukumar alhazai da EFCC ta yi a kwanakin baya kan zargin almundahana a aikin Hajjin na bara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com