Gumi Ya Sauya Shawara game da Mataki kan Lauya, Ya Kare Haduwarsa da Ƴan Bindiga
- Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya kuma yin magana kan ganawa da yan bindiga a Arewacin Najeriya
- Sheikh Gumi ya bayyana cewa duk ganawarsa da ‘yan bindiga ta kasance ne tare da jami’an gwamnati da ‘yan sanda
- Malamin ya fadi haka ne bayan zargin wani lauya da ya yi masa batanci da cewa yanzu ya fayyace kalamansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Shahararren malamin addinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi magana kan ta'addanci a Arewacin Najeriya.
Gumi ya bayyana cewa duk wata ganawa da ya taba yi da ‘yan bindiga ya yi ta ne tare da jami’an ‘yan sanda, da na gwamnati na jiha da na yankin.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a yau Asabar 8 ga watan Nuwambar 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya faru tsakanin lauya da Gumi
Gumi ya yi wannan bayani ne a ranar Asabar, yayin da yake mayar da martani kan wata barazanar daukar matakin doka da ya yi kan lauyan kare hakkin dan Adam, Malcolm Emokiniovo Omirhobo.
Wannan masanin shari'a ya nemi a binciki babban malamin fikihun kan zarge-zargen ta’addanci.
Sheikh Gumi ya ce bayanin da Omirhobo ya sake yi ya bayyana cewa maganarsa ba zargi ba ce, amma kira ne na bincike wanda kundin tsarin kasa ya amince da shi.
Sai dai Gumi ya nuna bacin ransa cewa, duk da kasancewar Omirhobo lauya ne, amma yana nuna son kai da rashin zurfin tunani wajen kiran a bincike shi.
A cewarsa:
“Ba ni taba zuwa wajen makiyaya masu dauke da makamai ba sai tare da jami’an tsaro, jami’an jihar da na yankin da abin ya shafa.”
Ya ce yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa da shawarwari kan yadda za a kawo karshen rikicin da ake fama da shi ba tare da tsoron ra’ayoyin duniya ba.

Kara karanta wannan
'Abin da zan faɗawa Trump ido da ido, idan na haɗu da shi': Barau Jibrin ya fusata

Source: Twitter
Gumi ya magantu kan hare-haren yan bindiga
Gumi ya bayyana cewa bincikensa ya gano cewa ‘yan bindigar sun dauki makamai ne saboda rashin adalci da suka fuskanta daga al’umma, kuma suna yakin kare rayuwarsu.
Ya ce yawancin kudin fansa da ake karba daga wadanda aka sace su ke tallafa musu, amma sun nuna aniyarsu ta daina yaki idan aka tabbatar musu da tsaro.
Gumi ya ce ‘yan bindigar sun bambanta da Boko Haram da IPOB, saboda suna neman zaman lafiya ne ba kamar sauran ba.
Masu suka sun dade suna zargin Gumi da goyon bayan ‘yan bindiga saboda kira da yake yi ga gwamnati da ta shiga tattaunawa da su domin kawo karshen rikice-rikicen kasar.
Sheikh Gumi ya fadi dalilin hare-haren yan bindiga
Mun ba ku labarin cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi karin haske game da dalilin da ya sa mafi yawancin 'yan bindiga ke kai hare-hare a sassan Najeriya.

Kara karanta wannan
Rikici tsakanin lauya da Sheikh Gumi ya canja salo, ana shirin dangana wa ga kotu
Malamin Musuluncin ya bayyana 'yan bindigar na kai hare-hare ne matsayin daukar fansar abin da aka yi masu.
Ya jaddada bukatar gwamnati na kiran zaman tattaunawa da ƴan bindiga domin samar da zaman lafiya mai dorewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
