'Yan Ta'adda Sun Fille Kan Shugaban CAN a Adamawa? 'Yan Sanda Sun Yi Bayani
- An yada wani rahoto mai ikirarin cewa 'yan ta'adda sun yi wa shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihar Adamawa kisan gilla
- Rahoton da aka yada dai ya nuna cewa an yi wa shugaban na CAN kisan gillar ne ta hanyar fille masa kai har sai da ya bar duniya
- Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta fito ta yi martani kan rahoton da aka yada a daidai lokacin da ake ci gaba da batun zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta yi magana kan rahotannin da ke cewa 'yan ta'adda sun kashe shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihar.
Rundunar 'yan sandan ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa an kashe shugaban na CAN a jihar ta hanyar yanke masa kai.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka, Trump ya ga ta kansa da 'yan shi'a suka fito zanga zanga a jihar Kano

Source: Facebook
An musanta batun kisan shugaban CAN
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton jaridar Vanguard ya ambato kungiyar CAN reshen Adamawa na musanta batun kisan shugabanta.
Jita-jitar dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da batun zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Zargin kisan Kiristocin dai ya jawo shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kawo hari Najeriya idan gwamnati ba ta dauki matakin da ya dace ba.
Me 'yan sanda suka ce kan kisan shugaban CAN?
A cikin wata sanarwar, rundunar ta bayyana wannan labarin da aka wallafa daga wani shafin Facebook mai suna “Lionman Lioni” a matsayin karya, mai cike da mugunta, kuma mai nufin tayar da hankula da rikicin addini a jihar.

Kara karanta wannan
Zargin ta'addanci: Kotun tarayya ta saka ranar yanke hukunci a kan shari'ar Nnamdi Kanu
Sulaiman Nguroje ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Dankombo Morris, psc (+), ya tabbatar cewa babu wani abu makamancin hakan da ya faru a ko’ina cikin jihar Adamawa.
“Babu wani rahoton kisan kai ko yankan kai da aka samu a jihar Adamawa. Wannan labarin ƙarya ne kuma manufarsa ita ce tada hankalin jama’a."
- SP Sulaiman Nguroje
Kwamishinan ya roƙi jama’a su yi watsi da wannan labari na bogi tare da tabbatar da gaskiyar kowane labari daga majiyoyi masu sahihanci kafin yada shi.
Ya kuma tabbatar cewa an kaddamar da bincike don gano da kuma gurfanar da wadanda ke da hannu wajen yada labarin na karya da nufin tada hankalin jama’a.

Source: Original
'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Delta sun cafke wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Abaniwonda Olufemi, ya ce an cafe wani mutum mai shekaru 60 da wasu mutane biyu kan zargin yin garkuwa da mutane tare da karɓar kudin fansa.
CP Abaniwonda Olufemi ya tabbatar da cewa dukkan waɗanda ake zargi suna hannun rundunar yanzu, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
