Akwai Matsala: An Gargardi Gwamnonin Jihohi 8 Su Shirya kafin Amurka Ta Kawo Farmaki Najeriya
- Wata kungiyar yarbawa (AYDM) ta ja hankalin gwamnonin Kudu maso Yamma da na Kogi da Kwara kan barazanar da Amurka ta yi
- Kungiyar ta bukaci gwamnonin su fara shirin tunkarar abubuwan da ka iya biyo baya idan sojojin Amurka sun farmaki yan ta'adda a Najeriya
- AYDM ta kuma soki wasu 'yan siyasa da shugabanni, wadanda suka yi fatali da yunkurin Amurka na kawo dauki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Kungiyar Yarbawa ta Alliance for Yoruba Democratic Movements (AYDM) ta gargadi gwamnonin jihohi takwas kan yiwuwar Amurka ta kawo farmaki Najeriya.
AYDM ta gargadi wadannan gwamnoni su shirya tunkarar tasirin abin da zai biyo baya idan gwamnatin Amurka ta kawo farmaki Najeriya kamar yadda Shugaba Trump ya yi barazana.

Source: Twitter
Gwamnoni 8 da AYDM ta yi wa gargadi
Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnonin da kungiyar ta yi wa gargadi sun hada da na jihohin Legas, Ekiti, Ogun, Ondo, Osun da Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran jihohin su ne Kogi da Kwara, inda kungiyar ta nemi ta fara shirin tunkarar abin da zai biyo baya idan Amurka ta kawo farmaki a Najeriya.
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Juma’a mai dauke da sa hannun sakatare janar, Poloola Ajayi, da Sakataren Yaɗa Labarai, Suleiman Sanusi.
AYDM ta ce irin wannan hari na iya tursasa ‘yan ta’adda barin Arewa su koma yankin Yammacin ƙasa, musamman idan Amurka ta kai musu farmaki.
AYDM ta ba gwamnatoci shawara
Kungiyar AYDM ta ce wadanda ke magana kan kare martabar Najeriya, su na mantawa cewa shugabannin kasar sun dade suna lalata wannan martaba ta hanyar rashawa, magudin zabe da goyon bayan ‘yan ta’adda.
“Gaskiya ita ce, Najeriya ba ta da ƙarfin da za ta hana Amurka kawo irin wannan hari.
"Abin da ya fi dacewa shi ne gwamnatocin jihohi da tarayya, su fara shirin yadda za su fuskanci illolin hakan ba tare da taba mutuncin Yarbawa ba,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya
Kungiyar ta ce ko da yake ana kashe Kiristoci da yawa a Najeriya, Musulman Yarbawa da na Tsakiyar ƙasa ma suna fama da ta’addanci a kasar nan.
Kungiyar AYDM ta soki yan siyasa
AYDM ta bukaci gwamnonin Yammacin Najeriya su yi aiki tare da kungiyoyin kare muradun Yarbawa wajen tattara bayanan sirri da kare al’ummomin yankin daga ‘yan ta’adda.
Ta kuma zargi wasu shugabannin siyasa da na addini da rashin gaskiya da son kai, tana cewa sun ki amincewa da shirin Amurka ba tare da bayar da wata mafita mai ma’ana ba.

Source: Getty Images
Adeboye ya yi magana kan barazanar Amurka
A wani labarin, kun ji cewa babban limamin cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta daukar mataki kafin Amurka ta kawo farmaki Najeriya.
Malamin cocin ya shawarci shugaban kasa ya nemi hanyar lallaba Trump ya ɗaga matakin da yake shirin ɗauka da tsawon kwanaki 100.
Faston ya kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta tona asirin masu daukar nauyin ta’addanci da ‘yan tawaye a ƙasar, ba tare da la’akari da matsayin da suka taka ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
