TAF Africa Ta Yi Magana kan Tsaro yayin da ake Zaben Gwamnan Anambra

TAF Africa Ta Yi Magana kan Tsaro yayin da ake Zaben Gwamnan Anambra

  • An fara samun bayanai game da yanayin tsaro yayin da jama'a ke cigaba da kada kuri'a a zaben gwamnan Anambra
  • Wani mai sa ido daga kungiyar TAF Africa ya ce jama’an Anambra su kwantar da hankulansu dangane da tsaro
  • Rahoto ya ce ya yi kira ga jami’an tsaro da su guji yin abin da zai iya zama barazana ga kwanciyar hankalin masu zabe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - A yayin da zaben gwamnan jihar Anambra ke gudana, wani mai sa ido daga kungiyar farar hula mai suna TAF Africa, Jake Epelle, ya yi magana kan tsaro.

Ya bayyana cewa al’ummar jihar suna gudanar da harkokinsu cikin natsuwa tare da ƙarancin fargaba kan tsaro.

Zaben gwamnan jihar Anambra
Yadda ake gudanar da zaben gwamna a Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

A hira da Channels TV, Epelle ya ce duk da yawaitar jami’an tsaro a fadin jihar, jama’a suna bayar da hadin kai domin tabbatar da cewa ba a samu tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

INEC na fuskantar matsin lamba kan zaben Anambra, hukumar ta yi magana kan BVAS

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TAF Africa ta yabi mutanen Anambra

Epelle, wanda shi ne wanda ya kafa kungiyar TAF Africa ya ce yanayin jihar ya nuna yadda mutanen Anambra ke da himmar kare juna da kuma son zaman lafiya a lokacin zabe.

Ya ce:

“Halin zaman lafiya da jama’ar Anambra ke nunawa abin a yaba ne. Kowa na kokarin tabbatar da cewa ba a zubar da jinin wani ba.”

Ya bayyana cewa kungiyar su ta ziyarci wurare da dama don sa ido kan harkokin zabe, inda suka lura da natsuwa da tsari wajen gudanar da komai.

Sai dai ya yi gargadin cewa yawan jami’an tsaro da ke bakin aiki na iya zama barazana idan ba a kula da yadda ake amfani da su ba.

Bukatar jami’an tsaro su yi adalci

A cewar Epelle, kasancewar jami’an tsaro a wurin zabe abu ne mai kyau, amma wajibi ne su guji yin abin da zai kawo tarnaki ga aikin da suke yi.

Kara karanta wannan

INEC ta dauki matasa 24000 aikin zabe, Yiaga ta hango abin da zai faru a Anambra

Zaben gwamnan Anambra
Masu kada kuri'a a zaben gwamnan Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook
“Jami’an tsaro su tabbatar da cewa ba sa nuna son rai. Abin da ke jawo rikici shi ne lokacin da jam’iyyun adawa suka ga an nuna bambanci,”

- Inji shi

Ya bayyana cewa ya gana da ‘yan sanda a wani taron tattaunawa, inda suka tabbatar da cewa za su yi aikinsu ba tare da nuna bambanci ba.

Yawan masu kada kuri’a da ‘yan takara

Rahoton INEC ya nuna cewa masu kada kuri’a 2,802,790 ne ake sa ran su kada kuri’a a rumfunan zabe 5,718 da ke cikin kananan hukumomi 21 na jihar.

Cikin fitattun ‘yan takarar akwai gwamna mai ci, Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA, Nicholas Ukachukwu na APC, George Moghalu na LP, da kuma Jude Ezenwafor na PDP.

Ana kwallo a filin zaben Anambra

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu matasa sun tafi filin kwallo yayin da ake zaben gwamna a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

'Ba Fulani ke yi ba': An gano wadanda ke kashe al'umma a Kudancin Najeriya

Legit Hausa ta gano cewa matasan na kwallo ne a kusa da wata rumfar zabe da jami'an hukumar INEC ke aiki.

Masu sayar da abinci da dama sun kasa kaya a rumfunan zabe domin neman taro da sisi da saukakawa masu kada kuri'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng