Abu Ya Tsananta: Mutane Sun Tsere daga Gidajensu kan Hare Haren 'Yan Bindiga a Kano
- 'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutanen da ke rayuwa a wasu kauyukan da ke kan iyaka a jihar Kano
- Hare-haren na bindga sun kara muni ne biyo bayan farmakin da sojoji ke kai musu a jihohin da ke makwabtaka da Kano
- Lamarin dai ya tilastawa mutanen kauyuka da dama zama 'yan gudun hijira bayan da suka tsere daga gidajensu don tsira da rayukansu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Mazauna kauyukan da ke kan iyaka a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano sun tsere daga gidajensu bayan jerin hare-haren ’yan bindiga.
Hare-haren na 'yan bindiga ya tilastawa mutanen barin matsugunansu, lamarin da ya bar wasu kauyuka gaba ɗaya babu mutane.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce da dama daga cikin mutanen da abin ya shafa yanzu suna neman mafaka a kauyen Faruruwa da garin Shanono.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama dai sun bar gidajensu, gonaki da dabbobinsu saboda tsoron farmakin ’yan bindiga.
Bayan yarjejeniyar sulhu da aka yi a wasu sassan jihar Katsina da kuma farmakin sojoji da ake gudanarwa a wasu jihohin Arewa maso Yamma, ’yan bindiga daga waɗannan wurare suna tserewa zuwa kauyukan jihar Kano da ke iyaka da yankunan da ake kai wa farmaki.
'Yan bindiga na kai hare-hare
Wani da ya yi kaura daga kauyen Santar Abuja, mai suna Sabiu Bako (ba sunansa na gaskiya ba), ya bayyan cewa ’yan bindiga sun addabi yankin, suna tsoratar da jama’a ba dare ba rana.
“Tun daga Asabar har zuwa Alhamis ba mu kasance a gida ba. Muna cikin fargaba saboda suna iya dawowa kowane lokaci. Muna yawan taruwa a Faruruwa domin neman tsira ko mu koma garin Shanono."
“Dukkan kauyenmu yanzu babu kowa. Wasu suna kwana a tituna, wasu a gonaki ko a gidajen mutane. Ni ina da mata huɗu da ’ya’ya 24, duk suna cikin gidajen mutane a Faruruwa."
- Sabiu Bako
Mutane sun koma 'yan gudun hijira
Ya ce mazauna kauyuka da dama ciki har da Unguwar Kudu, Yan Kwada, Malamai, Santar Abuja, Unguwar Tsamiya, Goron Dutse, Tudun Fulani da Kulki, duk sun bar gidajensu, sun bar dukiyoyinsu da gonakinsu.
Ya bayyana cewa wasu matasa kaɗan ne ke komawa da rana don kula da gonaki sannan su dawo wajen da suke samun mafaka kafin yamma.
Wani shugaban al’umma a Faruruwa da ke karɓar ’yan gudun hijira ya ce gidansa ya cika, mutane sun yi yawa sosai.
Wani babban dattijo a yankin ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin tashin hankali, inda ya ce kauyuka gaba ɗaya sun watse, mutane na tserewa kullum domin neman tsira.
Ya tabbatar da cewa a yanzu haka daga kauyen Santar Abuja kadai akwai iyalai 276 da ke neman mafaka a Faruruwa.

Source: Facebook
An yabawa jami'an tsaro
Sai dai mazauna yankin sun yaba da karin sintirin jami’an tsaro, wanda ya rage yawan hare-haren cikin kwanaki biyu da suka wuce.
“Muna godiya da kasancewar jami’an tsaro a yankin. Da ba don su ba, ba mu san abin da zai same mu ba."
- Wani dan gudun hijira
Yakamata gwamnati ta tashi tsaye
Wani mazaunin Kano mai suna Ibrahim Zulkiful ya shaidawa Legit Hausa cewa ya kamata gwamnati ta tashi tsaye domin daukar matakin da ya dace.
Ya nuna cewa hare-haren babbar barazana ce ga mutanen da ke rayuwa a yankunan.
"Wajibi ne kan gwamnati ta tashi tsaye domin magance matsalar nan kafin ta zama babba."
"Sauran wuraren da ake fama da matsalar tsaro duk kusan da haka aka fara har abin yanzu ya ta'azzara."
- Ibrahim Zulkiful
Kisan 'yan bindiga: Barau ya yabawa sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yabawa dakarun sojojin Najeriya.
Sanata Barau Jibrin ya yabawa dakarun sojojin ne kan nasarar da suka samu ta hallaka 'yan bindiga kusan 20 a jihar Kano.
Ya kuma bukaci al'ummar yankunan da abin ya shafa da su kara sanya ido kan duk wani motsin da ba su yarda da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


