Lamari Ya Girma: Amurka Ta Soke Bizar Mutane 80,000, ciki har da 'Yan Najeriya
- Amurka ta soke biza sama da 80,000 ta ‘yan ‘yan Najeriya da wasu kasashe, a wani mataki na tsaurara dokokin shige da fice
- Rahoto ya nuna cewa soke bizar ya shafi mutanen da suka aikata laifuffukan sata, cin zarafi, da kuma tuka mota cikin maye (DUI)
- Matakin na daga cikin shirye-shiryen Shugaba Donald Trump na kare hana shigowar wadanda ake zargi da tsattsauran ra’ayi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Gwamnatin Amurka ta sanar da soke fiye da biza 80,000, ciki har da ta ‘yan Najeriya, a wani babban shiri na tsaurara dokokin shige da fice.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoba, 2025.

Source: Getty Images
Amurka ta soke bizar mutane 80,000
A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin ma'aikatar na X, Amurka ta ce matakin zai kare tsaron kasa da muradun Amurkawa, karkashin manufar “alkawarin da aka yi, aka cika shi.”
Rahoton hukumar ya nuna cewa mutane 16,000 sun rasa biza saboda tuka mota cikin maye, 12,000 saboda duka ko kai hari, yayin da 8,000 suka rasa takardunsu saboda sata.
Ma'aikatar ta kuma bayyana cewa an soke bizar da ta ba wasu saboda dangantaka da ta’addanci, aikata laifuffukan tsaro, ko karya sharuddan bisa.
Sauyin tsare-tsare na bada bizar Amurka
Wani babban jami’in ma’aikatar wajen Amurka, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya ce wadannan laifuffuka uku – cin zarafi, sata da tuki cikin maye – su ne dalilin soke rabin bizar da aka yi a bana.
Ya kara da cewa wannan tsauraran mataki na cikin shirin Shugaba Donald Trump tun daga farkon mulkinsa domin rage shige da fice ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin Amurka ta kuma dawo duba bayanan shafukan soshiyal midiya na masu neman biza don gano masu ra’ayoyin da za su iya zama barazana ga tsaron kasa, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya

Source: Twitter
Tsauraran matakai kan ra’ayoyin siyasa da tsaro
A watan Mayu, sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa an soke dubban biza saboda ayyukan da suka sabawa manufofin waje na Amurka.
Ya ce an umarci jakadu su kula da masu neman biza da ke nuna ra’ayoyin adawa da manufofin Amurka ko goyon bayan ƙungiyoyin da ake zargi da ta’addanci.
Gwamnatin Amurka ta kuma yi gargadi cewa masu biza da green card na iya fuskantar kora daga kasar idan suka nuna goyon baya ga Falasɗinu ko suka soki Isra’ila yayin rikicin Gaza.
Soke bizar mutane 80,000 dai ta zama daya daga cikin manyan matakan da ma’aikatar ta dauka cikin shekaru, wanda ya nuna karfin manufofin Trump wajen tsaurara shige da fice.
Sharadin Soyinka na karbar bizar Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Farfesa Wole Soyinka ya ce shugaban Amurka Donald Trump yana da halayen kama-karya irin na tsohon shugaba Uganda.
Fitaccen marubucin ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan matakin da Amurka ta dauka na soke bizarsa, ba tare da ya aikata wani laifi ba.
Soyinka ya ce zai karɓi bizar Amurka ne kawai idan gwamnatin Trump ta fahimci cewa an yi masa rashin adalci, ba don ya aikata wani laifi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

