"Abin da Ya Sa Ƴan Bindiga Ke Farmakar Ƴan Najeriya," Gumi Ya Fito da Wani Zance
- Sheikh Ahmad Gumi ya yi karin haske game da dalilin da ya sa mafi yawancin 'yan bindiga ke kai hare-hare a sassan Najeriya
- Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya bayyana 'yan bindigar na kai hare-hare ne matsayin daukar fansar abin da aka yi masu
- Malamin ya jaddada bukatar gwamnati na kiran zaman tattaunawa da ƴan bindiga domin samar da zaman lafiya mai dorewa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana dalilin da ya sa ƴan bindiga ke kai hare-hare a sassan Najeriya.
Sheikh Gumi ya ce haka kurum, wadanda ake zargin ba sa daukar makami su farmaki mutane, "dole sai da wani dalili mai karfi."

Source: Facebook
'Dalilin 'yan bindiga na farmakar mutane' - Gumi
A zantawarsa da Trust TV a ranar Juma'a, 7 ga Nuwamba, 2025, malamain addinin da ke da zama a Kaduna, ya ce 'yan bindiga na kai harin daukar fansa ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa yawancin 'yan bindigar na kai hare hare kan 'yan Najeriya ne matsayin daukar fansar wani laifi da suke ganin an yi masu.
Ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani kan yunkurin shugaban Amurka Donald Trump na kawo hari Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.
Sheikh Gumi ya sake jaddada bukatar gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da ƴan bindiga, yana mai cewa hakan shi ne “tushen samun zaman lafiya mai dorewa.”
Gumi ya bukaci a tattauna da ƴan bindiga
Fitaccen malamin addinin ya bayyana cewa:
“Ƴan bindiga ba kamar 'yan kungiyar IPOB bane waɗanda suka ƙi yarda su tattauna da gwamnati. Idan aka kira 'yan bindiga don a yi tattaunawar zaman lafiya, za su zo.
"Ba sa kai hari ba tare da wani dalili ba. 'Yan bindiga na kai hare-hare ne don daukar fansa. Idan aka kira su zuwa teburin sasanci, za su zo."

Kara karanta wannan
Zargin bai wa 'yan ta'adda kudi: Gwamnatin Kaduna ta fadi yadda ta taimaki 'yan bindiga
A kwanakin baya, Punch ta rahoto cewa Gumi ya ce gwamnatoci na duniya ma suna yin sulhu da ƙungiyoyin da suka taɓa kiransu da “yan ta’adda,” don haka babu laifi idan Najeriya ta yi hakan.
A cewar malamin addinin:
“An samu zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Hamas — wadanda aka kira ‘yan ta’adda — kuma Amurka ta shiga tsakani. To me ya hana mu yin haka a Najeriya?”
Gumi ya ƙara da cewa:
“Ku yi sulhu da ƴan bindiga, mu samu zaman lafiya. Ba dole sai an yake su ne za a samar da kwanciyar hankali ba.”

Source: Facebook
Misali da sulhun Isra’ila da Hamas
Sheikh Gumi ya jaddada cewa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Isra’ila da Hamas a ce ta taimaka aka saki fursunonin Falasɗinu da kuma ‘yan Isra’ila da aka kama.
Ya ce wannan misali ne da ke nuna cewa ana iya samun mafita ko a rikice-rikicen da suka dade ana fama da su ta hanyar tattaunawa.
A cewar Gumi, idan ana iya yin sulhu a irin wannan rikici na duniya, to babu dalilin da zai hana gwamnatin Najeriya yin haka da ƴan bindigar cikin gida.

Kara karanta wannan
'Sai an biya kudi ake ganin Tinubu a Aso Villa,' Sanata Ndume ya yi sabuwar bankada
Kalli bidiyon a nan kasa:
'Musulmi zai mulki Amurka' - Gumi
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce wata rana Musulmi zai zama shugaban kasar Amurka.
Hasashen Gumi ya zo ne bayan nasarar Zohran Mamdani da ya zama Musulmin farko da ya lashe kujerar magajin garin New York.
Kalaman malamin sun haifar da ce-ce-kuce a soshiyal midiya, inda wasu ke ganin cewa Gumi yana nufin Musulmai za su samu damar samun manyan mukamai a kasashen Yamma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
