Momodu Ya Fadi Manyan Kasa 3 da Ya Kamata Tinubu Ya Turawa Trump
- Dele Momodu ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tuntubi ‘yan Najeriya masu tasiri domin tattaunawa da Donald Trump
- Hakan na zuwa ne bayan Trump ya yi barazanar kawo hari Najeriya bisa zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi ba tare da hujja ba
- Momodu ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan tsarin diflomasiyya domin kare mutuncin Najeriya a idon duniya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Fitaccen dan jarida kuma jigo a jam’iyyar ADC, Dele Momodu ya shawarci shugaba Bola Ahmed Tinubu kan barazanar Donald Trump.
Momodu da ya nemi hada kai da ‘yan Najeriya masu kima da suna a duniya domin tattaunawa kai tsaye da shugaban Amurka, Donald Trump.

Source: Facebook
Da yake magana a ranar Juma’a a Channels Television, Momodu ya bukaci shugaba Tinubu da ya daina kallon lamarin a matsayin siyasar cikin gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawarar Dele Momodu ga Bola Tinubu
Momodu ya jaddada cewa Najeriya tana da mutane masu basira da tasiri a duniya, wadanda za su iya amfani da kwarewarsu da dangantakarsu wajen warware wannan rikici.
Ya ce:
“Najeriya tana da dimbin mutane masu hazaka da kwarewa a duniya. Akwai ‘yan Najeriya da ke da manyan mukamai da alaka a kasashen duniya.
"Shawara ta ita ce shugaba kada ya dauki wannan lamari a matsayin siyasa ta jam’iyya kawai. Ya tuntubi irin wadannan mutane, ko suna jam’iyyarsa ko a’a.”
Ya kara da cewa dogaro da masu magana a fadar shugaban kasa ba zai wadatar ba wajen warware matsalar, saboda irin lamarin yana bukatar mai isar da sakon da duniya ke girmamawa.
Da gaske Trump ya ke yi inji Momodu
Momodu ya yi tsokaci kan bidiyon da Trump ya sake wallafawa inda ya jaddada matsayar Amurka kan Najeriya, yana mai cewa shugaban Amurka yana daukar lamarin da matukar muhimmanci.
Punch ta wallafa cewa ya ce:
“Ina ganin Trump yana da hujjojin da ya dogara da su. Yana ganin gwamnati ba ta kokari, kuma yana tsoron cewa za mu yi wasa ko sakaci.”
A cewarsa, wannan ne dalilin da ya sa ake bukatar tsofaffin shugabanni da manyan dattawan kasa su shiga tsakani domin bayar da shawarar da za ta tabbatar da mutuncin Najeriya a duniya.
Manyan kasa 3 da Momodu ya ambata
Dele Momodu ya ambaci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, tsohon sakatare janar na kungiyar kasashen renon Birtaniya, Emeka Anyaoku a matsayin wadanda za su iya shiga tsakani.
Haka zalika ya ambaci tsohon hafsan sojojin kasa, Janar Theophilus Danjuma a matsayin mutanen da Tinubu ya kamata ya tuntuɓa.

Source: Getty Images
Ya ce wadannan dattijai suna da gogewa da kima a fannin diflomasiyya, kuma za su iya taimakawa wajen sassauta tsamin dangantaka da Amurka.
Gogaggen 'dan jaridar ya kuma musanta rade-radin da ke cewa ‘yan adawa ne suka haddasa wannan matsin lamba daga Amurka, yana mai cewa:
“Ta ya ya jam’iyyar adawa da har yanzu ke kokarin tsara kanta za ta samu damar zuwa Washington? Na karanta cewa wani Fasto daga Benue ne ya fara gabatar da korafi.”
APC ta tura wasika majalisar Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen Amurka ta rubuta wasika zuwa ga majalisar kasar kan barazanar shugaba Donald Trump.
Shugaban APC reshen Amurka ya ce zargin da Trump ya yi ba gaskiya ba ne domin an cakuda lamarin baki daya.
Jam'iyyar ta bukaci gwamnatin Amurka ta bi hanyar diflomasiyya wajen warware matsalar maimakon nuna karfin soja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


