Abubuwa 8 da ba Ku Sani ba game da Jihar Anambra da Ake Shirin Zaben Gwamna
- Jihar Anambra da ake kira “Hasken Najeriya” ta kasance cibiyar al’adu, kasuwanci da tarihi yayin da zaben gwamna na 2025 ke kara karatowa
- Jihar ta yi fice wajen samar da manyan shugabanni da masana, tun daga Dr. Nnamdi Azikiwe har zuwa masana’antun Nnewi da kasuwar Onitsha
- A gobe ne ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar da za a fafata tsakanin gwamna mai ci, Charles Chukwuma Soludo da sauran 'yan takara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka - Jihar Anambra, wacce ake kira “Hasken Najeriya,” na daga cikin jihohin da suka fi kima a fannin al’adu, kasuwanci da ilimi a Najeriya.
A yanzu haka ana ta shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a gobe Asabar 8 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan
Daga Obi zuwa Soludo: Yadda APGA ta rike wuta, ta mulki Anambra na tsawon shekaru 20

Source: Original
Muhimman abubuwa game da Anambra
Daga bayanan da muka samu a Wikipedia, jihar na alfahari da tarihin shugabanci, hikima da al’adar mutanen Igbo da suka kafa ginshiƙin cigaba a yankin Kudu maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta duba muku wasu muhimman abubuwa game da jihar Anambra a Kudu maso Gabashin Najeriya.
1. Asalin sunan Anambra
Sunan Anambra ya samo asali ne daga Kogin Anambra, wanda ake kira Omambala mai cike da tarihi.
Kogin ya kasance ginshiƙi ga harkokin sufuri, noma da kamun kifi tsawon ƙarni, yana da ma’anar tarihi da al’ada ga al’ummar da ke zaune a gefensa.
2. Jiha da ta kafa tarihi
Anambra na alfahari da kasancewa wurin da aka fara samun shugabanni masu tarihi a Najeriya.
Ita ce ta samar shugaban kasa na farko kuma babban gwamnan yanki da ake kira 'Governor-Janar, Dr. Nnamdi Azikiwe, wanda ya kafa tushen al’ada ta jagoranci da hazaka.
3. Cibiyar al’adun Igbo
Jihar Anambra na a matsayin zuciyar al’adun Igbo, inda bukukuwa, kiɗa da fasaha ke ci gaba, wanda ya kara tabbatar da irin zamantakewar da ake yi a tsakanin al'umma.
Dodannin gargajiya irin su Ijele da Odogwu suna wakiltar addinan gargajiya wanda ke nuna bambance-bambance da ake da su, haka nan, fasaha ya haɗa al’umma da kare tarihin da ya gabata kafin zamanin Turawa.
4. Babbar cibiyar kasuwanci
Jihar Anambra ta shahara da kasuwanci a nahiyar Afirka, kasuwar Onitsha ita ce babbar kasuwa a yammacin Afirka, kamar yadda muka tsamo a shafin Anambra News a Facebook.
Har ila yau, kasuwar Nnewi ta yi suna da masana’antar kera sassan motoci, wannan ya nuna basirar ‘yan Anambra wajen sana’a da kirkire-kirkire.
5. Dumbin tarihi kan masarautu
Kafin zuwan Turawa, Anambra ta kasance gida ga tsofaffin masarautu wanda ya kara tabbatar da irin yadda ta rike al'adu da muhimmanci.
Masarautar Nri ta fi fice, inda Eze Nri ke mulki da adalci da zaman lafiya a tsakanin mutanen Igbo gaba ɗaya.
Anambra, a taƙaice, ba kawai jiha bace, amma ginshiƙi ce ta al’adu, ilimi, da ci gaban mutanen Igbo da Najeriya baki ɗaya.
6. Gidan fitattun makarantu
Ilimi na da matukar muhimmanci a Anambra wanda hakan ne ma ya sanya jihar daya daga cikin jihohi da ke da masu ilimi a Najeriya.
Jihar na dauke da jami’o’i masu daraja kamar ta Nnamdi Azikiwe da Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu.
Wannan ya taimaka wajen samar da masana da shugabanni da dama masu ilimi idan aka kwatanta da wasu jihohi.
8. Muhimmancin Kogin Omambala
Baya ga muhimmancinsa a taswirar ƙasa, Kogin Omambala yana da tasiri a al’adu da addinin al’ummar jihar baki daya.
Mutanen da ke zaune kusa da shi na ganin kogin a matsayin alama ta albarka da haɗin kai a tsakanin mutanen yankin.

Source: UGC
Gwamna Soludo ya ba da hutun zaben Anambra
Mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ke yankin Kudancin Najeriya a gobe Asabar 8 ga watan Nuwambar 2025.
Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Chukwuma Soludo ta ayyana ranar hutu a yau Juma'a 7 ga watan Nuwambar shekarar 2025 domin ba ma'aikata damar zuwa yankunansu saboda su kada kuri'unsu.
A cikin sanarwar da aka fitar, an bukaci ma'aikatan da su ba da irin tasu gudunmawar wajen inganta tsarin dimokuradiyya tare da gargadin masu neman tayar da kayar baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


