Manoman Najeriya za Su Samu Naira Biliyan 250 domin Habaka Samar da Abinci

Manoman Najeriya za Su Samu Naira Biliyan 250 domin Habaka Samar da Abinci

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana sabuwar hanyar amfani da Naira biliyan 250 domin tallafawa kananan manoma da nufin karfafa samar da abinci a kasa
  • Ministan noman Najeriya, Abubakar Kyari, ya ce kudin na daga cikin shirin sabunta babban bankin noma da kuma inganta dabarun noma a kasar
  • Sanata Kyari ya bayyana cewa sun rungumi shirin uwar gidan shugaban kasa na kafa lambuna a kowane gida domin habaka samar da abinci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Gwamnatin tarayya ta sanar da kaddamar da asusun Naira biliyan 250 domin karfafa kananan manoma a fadin kasar nan.

Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani bangare na shirin gwamnati na tabbatar da isasshen abinci da kuma inganta harkar noma a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya kara yin kasa warwas a Najeriya', Minista ya bayyana dalili

Shugaba Bola Tinubu
Hoton shugaba Tinubu da motar noma a gona. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

The Sun ta ce ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan a wajen taron majalisar kasa ta noma da tsaron abinci karo na 47 da aka gudanar a jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kudin za su kasance kari ne ga Naira tiriliyan 1.5 da gwamnati ta ware don sake karfafa Bankin Noma (BOA) domin tallafawa manoma.

Ana shirin habaka noma a Najeriya

Kyari ya ce gwamnati ta kaddamar da shirye-shirye ciki har da shirin noman zamani na Renewed Hope da kuma noman rani don noma a duk shekara a kan fili mai girman kadada 500,000.

The Guardian ta rahoto ya ce gwamnati tana aiki don saukaka samun kayan noma da rage farashinsu, tare da samar da horo kan hanyoyin noman zamani.

A cewarsa, shirin ya riga ya taimaka wajen karuwar alkama a yankunan da ake noman rani da kuma damuna a jihohin Filato, Taraba da Kuros Riba.

Gwamnati na karfafa mata da matasa

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya na fatan karya farashin taki da sauran kayan noma

Ministan ya ce gwamnati ta karfafa shirin ajiyar hatsi a jihohin Zamfara, Katsina, Nasarawa, Adamawa, Neja, Osun, Edo da Kwara domin tabbatar da wadatarsa da daidaita farashi a kasuwa.

Ya ce:

“Domin karfafa tsaron abinci da daidaita farashin kayan abinci, mun inganta yadda ake gudanar da ajiya a manyan rumbunan hatsi na kasa domin samun damar daukar mataki cikin gaggawa idan an samu karancin kayayyaki.”

Kyari ya ce an kaddamar da wani shiri na hadin gwiwa da kamfanin Heifer Nigeria don bunkasa cibiyoyin noma da matasa da mata ke gudanarwa a dukkan yankuna shida na kasar.

Sanata Abubakar Kyari
Ministan noma na kasa, Sanata Abubakar Kyari. Hoto: @SenatorAKyari
Source: Facebook

Haka kuma, ya ce gwamnati ta rungumi shirin “Every Home a Garden” na uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, don karfafa mata da sauran jama'a wajen noma a gidajensu.

Gwamnati na son karya farashin taki

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce ta kudiri niyyar saukar da farashin kayan noma, musamman taki a fadin kasar.

Ministan noma na kasa, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka yayin wani taro da aka yi a jihar Kadune game da bunkasa samar da abinci.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta kawo tsarin da jiragen kasa za su yi aiki a kowace jihar Najeriya

Ministan ya ce matakin na karkashin aniyar shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen kara habaka tattalin arzikin Najeriya da manoma a fadin kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng