Rana Zafi: Halin da Ake ciki bayan Kamfanin Wutar Lantarki Ya Kori Ma’aikata 800

Rana Zafi: Halin da Ake ciki bayan Kamfanin Wutar Lantarki Ya Kori Ma’aikata 800

  • Kamfanin wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya fara sallamar daruruwan ma’aikata bayan watanni na sake tsari a cikinsa
  • Rahotanni sun nuna cewa an fara shirin sallamar ma’aikata 1,800 amma an rage su zuwa 800 bayan tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikata
  • AEDC ta ce sallamar na cikin tsarin rage ma'aikata kuma za a biya hakkokinsu da abin ya shafe su bayan cikakken tantancewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kamfanin wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya fara sallamar ma’aikata domin kawo sauyi a tsarin ayyukansa.

An tabbatar da cewa kamfanin AEDC ya kori kusan mutum 800, a wani mataki da ake ganin zai kara jefa su cikin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar.

Kamfanin wutar lantarki a Abuja ya kori ma'aikata
Ofishin kamfanin wutar lantarki da ma'aikatansa a Abuja. Hoto: Abuja Electricity Distribution Plc.
Source: Facebook

Ma'aikata nawa aka yi niyyar kora a AEDC?

Rahoton Punch ya bayyana cewa sallamar ta fara ne a ranar Laraba, 5 ga Nuwamba, 2025, bayan watanni da dama na sake tsari a cikin gida.

Kara karanta wannan

'Ba Fulani ke yi ba': An gano wadanda ke kashe al'umma a Kudancin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin AEDC yana samar da wutar lantarki a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, Kogi, Neja da Nasarawa.

Majiyoyi daga cikin kamfanin sun shaida cewa tun farko an shirya a sallami ma’aikata 1,800, amma bayan doguwar tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikata, adadin ya ragu zuwa 800.

Wani ma’aikaci da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce:

“Tun farko suna so su sallami 1,800, amma bayan matsin lamba daga ƙungiyoyin ma’aikata sai aka rage zuwa 800.”
An kori ma'aikata 800 a kamfanin wutar lantarki
Taswirar birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da ma'aikata ke cewa kan lamarin

Wasu daga cikin ma’aikatan sun ce sun fara karɓar takardar sallama daga ranar Laraba, inda aka bayyana cewa shirin na cikin tsarin rage ma’aikata da kamfanin ke aiwatarwa.

Kamfanin ya ce duk waɗanda abin ya shafa za su biya kudin da ake binsu da suke da shi kamar haraji, bashi da sauran lamura kafin su karɓi hakkinsu.

AEDC ta kuma yaba da gudunmawar ma’aikatan yayin aikin su, tana masu fatan alheri a rayuwa, cewar Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

'Da gaske ne ana kisan kiyashi a Najeriya,' Jigon APC ya goyi bayan Donald Trump

Rahotanni sun nuna cewa wannan sallamar na iya kara matsa lamba ga ma’aikatan da suka rage, tare da kara haifar da rashin jin daɗi a tsakanin kwastomomin kamfanin, musamman a Abuja da jihohin da AEDC ke aiki.

Mai kula da hulɗa da kwastomomi na AEDC, Mista Kenechukwu Ofili, ya tabbatar da sallamar, yana mai cewa al’ada ce ta cikin gida, kuma ana bin matakan da aka cimma da ƙungiyoyin ma’aikata.

Gwamnatin Tinubu ka iya korar ma'aikata 3,000

A baya, an ji cewa gwamnatin tarayya ta sake sanya lokacin tantance wasu ma'aikata 3,598 saboda ba su samu zuwa tantancewar da aka yi a 2021 ba.

Hukumar kula da ma'aikata ta kasa ta bayyana cewa duk wanda ya gaza zuwa wannan tantancewar ya dauka ya rasa aikinsa ba tare da bata lokaci ba.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce za a tantance ma'aikatan ne daga ranar 18 zuwa 28 ga watan Agusta, 2025 domin tabbatar da sahihancin su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.