Gwamnatin Tarayya na Fatan Karya Farashin Taki da Sauran Kayan Noma

Gwamnatin Tarayya na Fatan Karya Farashin Taki da Sauran Kayan Noma

  • Gwamnatin tarayya ta ce za ta dauki mataki wajen dakile fasa-kwaurin kayayyakin gona zuwa cikin gida Najeriya
  • Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan yayin ziyara da wani taro da ya je jihar Kaduna
  • Ya ce gwamnati ta dukufa wajen ganin manoma sun samu kayayyaki kamar taki cikin sauki domin bunkasa noma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa kwamitin kula da tattalin arzikin kasa (EMT) na shirin daukar mataki mai tsauri kan matsalar fasa-kwaurin kayayyakin gona.

Wannan matakin, a cewar gwamnati, zai taimaka wajen daidaita farashin kayayyakin abinci da kuma kara tabbaci ga masu zuba jari a sashen sarrafa kayayyakin noma.

Sanata Abubakar Kyari
Ministan noma, Sanata Kyari. Hoto: @SenatorAKyari
Source: Twitter

Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan yayin wani taro a jihar Kaduna kamar yadda ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta kawo tsarin da jiragen kasa za su yi aiki a kowace jihar Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta saka ido a iyakoki

Sanata Kyari, wanda ya ziyarci cibiyoyin sarrafa kayayyaki na Olam, TMDK, da Tomato Jos, ya ce gwamnati tana saka ido kan masu shigo da kayayyaki ta barauniyar hanya.

A cewarsa, an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa manoman cikin gida sun ci gaba da zama masu karfi wajen gogayya da kayayyakin da ake shigowa da su daga waje.

Ministan ya ce:

“Kwamitin kula da tattalin arziki ya dauki batun kare iyakokin kasa daga fasa-kwauri da shigowa da abinci mai arha da muhimmanci sosai.”

Kyari ya ce manoma na karuwa

Ministan ya ce sha’awar masu zuba jari a harkar noma na karuwa sakamakon manufar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta samar da abinci.

Ya jaddada cewa matasa da mata masu gudanar da harkokin noma suna kara shiga fagen, abin da ya nuna karfin bangaren a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Bayan daura aure, matashi 'dan shekara 25 ya caka wa matarsa wuka har lahira a Sakkwato

“Mun ziyarci wata matashiya da ke da cibiyar sarrafa kayayyakin gona tare da kungiyar mata manoma, kuma hakan na nuna cewa mutane suna kara samun kwarin gwiwar zuba jari a harkar noma,”

- Inji shi

Kokarin rage farashin taki da kayan noma

Kyari ya kuma bayyana cewa gwamnati na kan hanyar rage farashin kayan shuka da noman rani a Najeriya.

Tribune ta rahoto ya ce:

“Za mu magance matsalar tsadar kayan noma. Sabunta rumbunan ajiya zai taimaka wajen kara kudin shiga a bangaren noma da kuma tallafawa manoma su ci gaba da noma cikin shekara baki daya,”

Game da takin ruwa da shugaban Tomato Jos ta koka da dakatar da shigowarsa, Kyari ya ce yana da amfani amma yana dauke da sinadarai da za a iya amfani da su wajen hada abubuwan fashewa.

Ministan noman Najeriya
Ministan noma tare da motocin noma da aka kawo Najeriya. Hoto: @SenatorAKyari
Source: Twitter

An yi taron kan harkar noma a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa an gudanar da taron NCAFS na kasa karo na 47 a jihar Kaduna domin bunksa noma a Najeriya.

Taron da ya hada mutane daga jihohin Najeriya ya mayar da hankali kan yadda za a bunkasa samar da abinci kasa baki daya.

Kara karanta wannan

TUC: Yan kwadago sun taso Gwamnatin Tinubu kan shirin kakaba harajin 15% kan fetur

Gwamnatin jihar Kaduna mai masaukin baki ta ce a shirye ta ke wajen tallafawa shirin domin bunkasa noma a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng