Isra'ila Ta Yi Kira ga 'Yan Najeriya yayin da ake Fargabar Barazanar Trump

Isra'ila Ta Yi Kira ga 'Yan Najeriya yayin da ake Fargabar Barazanar Trump

  • Jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi zaman lafiya da hadin kai a tsakanin addinai
  • Ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa tsakanin addinai da aka gudanar a Abuja, inda ya ce hadin kai shi ne tushen ci gaba
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da zama cikin fargaba game da harin da shugaban Amurka ya ce zai kawo Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zauna lafiya da juna.

Ya bukaci a zauna cikin fahimtar juna da girmama kowa, ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini ba.

Micheal Freeman, Netanyahu
Jakadan Isra'ila a Najeriya da Benjamin Netanyahu. Hoto: @M_S_Freeman
Source: Twitter

Punch ta ce ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin taron tattaunawa tsakanin addinai a Abuja, wanda ya hada da shugabannin Musulmi, Kiristoci da Yahudawa.

Kara karanta wannan

Trump: Najeriya ta gana da jakadun kasashe, an yi maganar Shari'ar Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jakadan ya ce tattaunawar ta zo a lokaci mai muhimmanci yayin da duniya ke fuskantar rikice-rikicen da suka samo asali daga rashin fahimta da rarrabuwar kai.

Bayanin jakadan Isra'ila a Najeriya

Jakadan na Isra’ila ya ce ba rashin rikici da tashin hankali ba ne kawai ya ke nuna ana zaman lafiya, ya ce girmamawa, tausayi da hada kai ne ke nuna ana zaman lafiya.

Ya kara da cewa:

“Zaman lafiya yana nufin zabar tattaunawa maimakon kiyayya da fahimtar cewa bambance-bambancenmu ne tushen karfinmu.”

Alaka tsakanin Isra’ila da Najeriya

Freeman ya bayyana cewa, duk da cewa akwai kalubale wajen zaman tare a Isra’ila, amma ana zaune da juna cikin fahimta.

Ya kwatanta Najeriya da Isra’ila yana mai cewa Najeriya kasa ce mai bambancin addinai da kabilu, amma tana da damar cigaba.

Benhamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila, Benhamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Freeman ya jaddada cewa:

“Zaman lafiya na gaskiya yana farawa daga matakin tushe – a makarantunmu, masallatai, coci-coci, da zukatan mutane.”

Kara karanta wannan

'Ba na jin tsoron Trump,' An samu sabani tsakanin Barau da Akpabio a majalisa

Martanin shugabannin addinai a taron

Imam Muhammed Ashafa daga bangaren Musulmi ya ce addinai na koyar da imani, amma tattaunawa tsakanin mabiya addinai tana kara hadin kai.

Vanguard ta rahoto ya ce:

“Lokacin da mabiya addinai suka hadu suka tattauna kan abubuwan da suka shafi rayuwar matasa, iyali da walwala, suna nunawa duniya cewa suna da hadin kai.”

Menachem Chitrik daga al’ummar Yahudawa ya yi kira ga shugabanni su zama abin koyi a gidajensu.

Peter Ogunmuyiwa na kungiyar Kiristocin Najeriya ya yaba da hadin kai da aka nuna, yana mai cewa idan muka yanke shawarar zama tsintsiya madaurinki daya, za mu samu zaman lafiya.

Amurka za ta kai hari Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake zargi da cin zarafin Kiristoci.

Gwamnatin Najeriya ta karyata zargin, tana mai cewa doka da kundin tsarin kasa suna kare kowane dan kasa ba tare da la’akari da addininsa ba.

Kara karanta wannan

An yi taron habaka noma da rage shigo da kayan abinci daga waje zuwa Najeriya

Trump ya ki yarda da martanin Najeriya tare da cewa zai kai hari domin kare Kiristoci, kuma sojojin Amurka sun fara tsara yadda za su kai farmaki kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng