Rai Bakon Duniya: Basarake kuma Kawun Mai Martaba Sarki Ya Rasu a Gombe
- Jihar Gombe ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar daya daga cikin sarakunanta wanda ya ba al'umma gudunmawa
- Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya tura ta’aziyyarsa kan rasuwar Hakimin Wuro Tale, Alhaji Adamu Yerima
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a yankin karamar hukumar Dukku da ke jihar Gombe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dukku, Gombe - Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya tura sakon ta'aziyya bayan rashin basarake a Gombe.
An bayyana cewa marigayin ya rasu ne a yankin karamar hukumar Dukku da ke jihar Gombe inda aka yaba da gudunmawar da ya bayar.

Source: Facebook
Pantami ya jajanta bayan rasuwar Hakimi a Gombe
Farfesa Pantami ya mika sakon ta'aziyyar a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 6 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pantami ya yi ta’aziyya ta musamman kan rasuwar Hakimin Wuro Tale, Alhaji Adamu Yerima, wanda Allah ya rasu a Dukku.
Ya kuma tura sakon ga dangin marigayi da Mai Martaba Sarkin Dukku, Alhaji Haruna Abdulqadir Rashid II.
Sheikh Pantami ya ce marigayin shi ne kawun Mai Martaba Sarkin Dukku wanda kuma shi ne Hakimin Wuro Tela a masarautar da ke jihar Gombe.

Source: Facebook
Addu'o'in da Pantami ya yi ga marigayin
Tsohon minisan ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya karɓe shi cikin aljannar Firdausi tare da iyayen da masoya da suka riga mu gidan gaskiya.
A cikin sanarwar, Pantami ya ce:
"Muna mika ta’aziyya ta musamman bisa rasuwar Hakimin Wuro Tale, Alhaji Adamu Yerima.
"Muna jajantawa dangin marigayi da kuma Mai Martaba Sarkin Dukku, Alhaji Haruna Abdulqadir Rashid II, bisa rasuwar kawunsa wanda kuma shi ne Hakimin Wuro Tale.
"Allah ya ji kansa, ya sanya shi cikin Jannatul Firdausi, tare da iyayenmu da masoyanmu da suka rigamu gidan gaskiya."
Martanin masu ta'ammali da kafofin sadawa
Mutane da dama sun taya Pantami jimami bayan rashin basaraken da aka yi a jihar Gomne inda suka ta yi masa addu'o'i.
Daga cikin wadanda suka yi martani akwai masu yi masa godiya bisa ta'aziyyar da ya yi musu a matsayinsu na yan karamar hukumar Dukku ko kuma kusanci da suke da shi da marigayin.
Gurama A Gurama ya ce:
"Amin ya Allah! mun gode sosai ya Sheikh."
Aliyu Moh D Rasheed:
"Amin ya Allah, muna godiya ya Sheikh, muna matukar godiya."
Lukman Umar:
"Amin, amma ba kawunsa ba ne, dan uwansa ne."
Pantami ya yi jimamin rasuwar Sheikh Jingir
A baya, kun ji cewa tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya shiga alhini bayan rasuwar malamin Izala, Sheikh Sa'idu Hassan Jingir, wanda aka sanar da rasuwarsa.
Pantami ya aika da ta’aziyya ga iyalan mamacin, almajiransa, ‘yan uwa da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir tare da shugabanni baki daya a Najeriya.

Kara karanta wannan
Daga shiga APC, Gwamna Diri ya yi wa Tinubu alkawarin kaso 99 na kuri'u a zaben 2027
Tsohon ministan ya ce marigayin ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen addini, don haka rasuwarsa babban rashi ne ga al’umma da daukacin Musulmi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

