Bayan Daura Aure, Matashi 'Dan Shekara 25 Ya Caka Wa Matarsa Wuka har Lahira a Sakkwato

Bayan Daura Aure, Matashi 'Dan Shekara 25 Ya Caka Wa Matarsa Wuka har Lahira a Sakkwato

  • Wani matashi dan shekara 25 a duniya, Sufiyanu Aliyu ya halaka matarsa da wuka yayin da sabani ya shiga tsakaninsu a jihar Sakkwato
  • Rundunar yan sanda ta kama wanda ake zargin tare da wukan da aka aikata laifin domin gudanar da bincike da gurfanar da shi a kotu
  • Kwamishinan yan sanda na reshen jihar Sakkwato, CP Ahmed Musa ya tabbatar wa jama'a cewa za a yi wa marigayiyar adalci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato ta kama wani matashi mai shekara 25, Sufiyanu Aliyu, bisa zargin caka wa matarsa wuka har lahira.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An lakadawa limamin masallacin Juma'a duka har ya mutu a Kwara

Ana zargin matashin ya kashe matarsa yar kimanin shekara 15, Suwaiba Abubakar Bawa, a kauyen Gwanyal da ke karamar hukumar Tangaza ta jihar Sakkwato.

Jihar Sokoto.
Hoton taswirar jihar Sakkwato Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta tattaro cewa lamarin, wanda ya faru a ranar 27 ga Oktoba 2025, ya girgiza mazauna yankin sakamakon yadda aka kashe yarinyar cikin zalunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa matashin ya kashe matarsa?

Rahotanni sun nuna cewa rigima ta shiga tsakanin Sufiyanu da Suwaiba matarsa, daga bisani rigimar ta rikide zuwa fada mai zafi.

Yayin wannan fadan ne matashin ya dauki wuka ya caka mata, wanda hakan ya zama silar mutuwarta nan take.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin ga menama labarai a wata sanarwa da ya fitar a Sakkwato.

'Yan sandan Sokoto sun kai dauki wurin

Ya bayyana cewa rundunar yan sanda ta samu kiran gaggawa daga wani da ya kai dauki wurin a kauyen da misalin ƙarfe 8:00 na dare a ranar da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yaba wa sojoji bisa nasarar da suka samu a Kano, ya tura sako ga Tinubu

“Ba mu yi wata-wata ba bayan samun rahoton, jami’anmu suka garzaya wurin da lamarin ya faru, suka kama wanda ake zargi a nan take, suka kwace wukar da ake zargin ya yi amfani da ita wajen aikata laifin,” in ji DSP Ahmad.

Kakakin 'yan sandan ya ce an kai gawar marigayiyar asibiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

DSP Ahmad Rufai ya kara da cewa wanda ake zargi ya amsa laifinsa a lokacin binciken farko da aka yi masa.

Wane mataki yan sanda suka dauka?

Ya ce yanzu haka an mika lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike kafin gurfanar da shi a kotu.

A halin yanzu, an riga an gurfanar da Sufiyanu Aliyu a kotu domin fara shari’a a kansa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Yan sandan Najeriya.
Hoton jami'an yan sanda a bakin aiki a Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Getty Images

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Musa, ya yaba da yadda jami’ansa suka hanzarta daukar mataki bayan samun labarin lamarin.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da adalci ga marigayiyar.

Magidanci ya kama matarsa da kwarto

A wani labarin, kun ji cewa wani magidanci ɗan shekara 38 a duniya ya ga abin mamakin a lokacin da ya dawo gida ba tare da sanar da matarsa ba.

Kara karanta wannan

Abba Kyari ya kafe a kotu, ya karyata zargin EFCC kan mallakar wasu kadarori

Mutumin mai suna, Mpanga da ke aiki a kamfani ya kama matarsa da kwarto a gadon aurensu, lamarin da ya daga masa hankali.

Tare da taimakon maƙwabta, aka kama kwarton mai suna, David Mbere zuwa ofishin 'yan sanda domin au dauki matakin da ya dace.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262