'Wane Hali Muke ciki,' Tsohon Hadiminsa Ya Nemi Tinubu Ya Yi Bayani kan Barazanar Trump
- Dr Hakeem Baba-Ahmad, ya bukaci shugaba BolaTinubu ya yi magana kai tsaye ga ‘yan Najeriya kan barazanar Donald Trump
- Ya ce yin haka zai rage fargaba da tashin hankali a kasar tare da tabbatar wa da jama’a cewa babu hatsari a gabansu kai tsaye
- Masu amfani da kafar X sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan wannan kira, wasu na goyon baya, sannan wasu kuma na sukarsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon mai ba da shawara ga shugaban kasa, Dr Hakeem Baba-Ahmad, ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi jawabi kai tsaye ga ‘yan Najeriya.
Ya bukaci haka ne kan barazanar shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi ikirarin cewa ana kisan gilla ga Kiristoci a Najeriya.

Source: Facebook
A cikin wani sako da ya wallafa a kafar X, Dr Hakeem ya ce lokaci ya yi da shugaban kasa zai fito fili ya kwantar da hankalin ‘yan kasar, maimakon barin maganar ta yadu ba tare da karin haske ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran Hakeem Baba Ahmad ga shugaba Tinubu
Dr Hakeem ya gargadi shugaba Tinubu da kada ya ziyarci Amurka a halin yanzu, yana mai cewa hakan zai rage darajar Najeriya.
A cewar Dr Hakeem:
“Ya kamata shugaba Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi kai tsaye kan barazanar Trump. Ya kwantar da hankula, ya rage fargaba, kuma ya tabbatar da cewa ba mu cikin barazana.
"Bai kamata ya tafi Amurka ba, hakan zai rage darajar kasar. Ya kamata ya nada jakadu a ofisoshin diflomasiyyar mu. Don Allah, Shugaba, ka yi jagoranci na gari!”
Kiran nasa ya biyo bayan kalaman Trump da ke cewa zai dauki matakin soja idan Najeriya ta kasa dakile hare-haren da ake zargin ana yi kan Kiristoci da Najeriya ta karyata.
Ra’ayoyin masu amfani da kafar X
Bayan sakon Dr Hakeem, masu amfani da kafar X sun rarrabu kan kiran da ya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu.
@Patrick03383733 ya rubuta cewa:
“Kana kan kuskure. Ba sai ya yi magana ba. Abin da ya kamata ya yi shi ne ya bi tsarin mulki wajen kare rayuka da dukiyar kowane ɗan Najeriya.
"Ya kamata kuma ya bayyana cewa babu wata doka da za a yi amfani da ita a Najeriya banda ta tsarin mulki.”

Source: Getty Images
Sai kuma @U_Victor26, wanda ya ce:
“Ba shi da wata kwarewa a harkar mulki. Har yanzu, babu kalma daya daga gare shi ga ‘yan Najeriya. Abin da muke gani kawai magoya bayansa ne suke maganganu a yanar gizo.
"Wane irin gibin jagoranci ne wannan?”
Wani mai amfani da kafar X @Uzochi_O ya ce:
“Ba zai iya ba! Yanzu da ake bukatar mulki na gaskiya, ya buya. Mun ji Trump sau hudu yana magana kan batun a cikin kwanaki biyar da suka gabata. Shugaban mu fa?”
Najeriya ta karyata zargin Trump
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaba Donald Trump ya zargi gwamnatin Najeriya da rashin kare Kiristoci daga kisan gilla.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta bayyana zargin a matsayin karya, tana mai cewa dukkan ‘yan kasar na fuskantar barazanar ta’addanci.
Duk da haka, Trump ya dage cewa ra’ayinsa gaskiya ne, yana mai cewa Amurka za ta dauki mataki da sauri idan Najeriya ta gaza.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


