TUC: Yan Kwadago Sun Taso Gwamnatin Tinubu kan Shirin Kakaba Harajin 15% kan Fetur
- Yan kwadagon Najeriya sun fara sukar shirin gwamnatin tarayya na kakaba harajin kaso 15 a man feturin da ake shigo da shi daga waje
- Shugaban TUC na kasa, Kwamared Festus Osifo ya ce harajin na iya karewa kan talakawa, wadanda ke fama da kuncin rayuwa
- Ya bukaci gwamnatin tarayya ta fito ta yi cikakken bayani kan yadda za ta aiwatar da harajin domin yan kasa su fahimci inda aka dosa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta TUC na kasa, Festus Osifo, ya yi gargaɗi kan halin da yan Najeriya za su shiga sakamakon kakaba harajin shigo da fetur.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na sanya harajin kaso 15 kan duk man fetur da dizal da za a shigo da shi daga kasashen ketare.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya

Source: UGC
Shugaban TUC ya ce wannan haraji zai iya kara tsananta halin wahala da kuncin rayuwa da yan Najeriya ke ciki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TUC ta hango yiwuwar tashin fetur
Da yake magana a shirin ‘TUC Half Hour’ na tashar Channels TV a ranar Laraba, Osifo ya bayyana cewa ƙungiyar na nazarin manufar tare da tuntubar masu ruwa da tsaki domin fahimtar tasirinta ta.
Ya ce, duk da cewa gwamnati na ganin harajin zai kare matatqun mai na cikin gida, amma zai iya kara tsadar fetur saboda har yanzu Najeriya na shigo da kusan kashi 70 na fetur daga waje.
“Ra’ayina shi ne a’a, a’a, a’a! Me yasa za a saka haraji alhali matatunmu ba sa tace adadin da muke bukata? Matatar Dangote tana bangaren yan kasuwa, wato tana da keɓantaccen haraji.
"Idan wannan harajin zai shafi masu shigo da mai daga waje, za su ɗora wa jama’a nauyin kuɗin ne kai tsaye.”
'Yan kwadago sun taso gwamnatin Tinubu
Osifo ya bukaci gwamnatin tarayya ta fayyace yanayin aiwatar da harajin, shin zai shafi masu shigo da mai daga ƙasashen waje ne kawai, ko har da masu saye a matatun cikin gida.
Ya ce rashin fitowa a yi bayani domin fahimtar da mutane zai iya haifar da rudani kuma a ƙarshe talakawa ne za su sha wahala a gidajen mai.
Shugaban TUC ya kuma jaddada cewa dole ne gwamnati ta nemi shawarwarin ƙungiyoyin ƙwadago da masana’antu kafin aiwatar da wannan haraji.

Source: Getty Images
Ya ce ƙungiyar TUC da ta PENGASSAN za su fitar da matsayinsu na ƙarshe bayan sun gama nazarin duk bayanan da suka dace.
"Babban manufarmu ita ce kare ma’aikata da talakawa daga ƙarin raɗaɗin tattalin arziki,” in ji shi.
Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta, wasu na ganin hakan ya yi daidai, wasu kuma na ganin harajin zai kara wa mutane kuncin rayuwa.
Wani ma'aikacin gwamnati, Abubakar Aliyu ya shaidawa Legit Hausa cewa harajin na iya zama abin alheri domin zai hana shigo da mai tun da akwai wuraren saya a cikin gida.
"ina ganin wannan abu me mai kyau tun da muna da matatun mai a cikin gida, hakan zai taimaka wajen jawo hankalin yan kasuwar fetur su dawo su rika sayen kaya a gida," in ji shi.
Sai dai wani matashi, Kabiru Ahmad ya ce idan har ba daina shigo mai aka yi ba, to fa wannan karin harajin zai kare ne a kan talakawa.
Farashin shigo da fetur ya sauka
A baya, kun ji labarin cewa farashin shigo da man fetur Najeriya daga ƙasashen katare ya sauka zuwa ₦829.77 a kan kowace lita.
Rahoto ya nuna cewa wannan sabon farashin ya ragu sosai idan aka kwatanta da na farashin matatar Dangote, wanda ke sayar da litar a kan ₦877.
Sai dai duk da haka, farashin litar fetur a gidajen mai a jihohin Lagos da Ogun bai canza daga ₦920 ba, alamar cewa farashin bai sauka a kasuwa ba tukuna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

