Femi Falana: Babban Lauya Ya Fallasa Trump kan Zargin Kisan Kiristoci

Femi Falana: Babban Lauya Ya Fallasa Trump kan Zargin Kisan Kiristoci

  • Babban lauya a Najeriya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya yi wa shugaban kasar Amurka, Donald Trump martani
  • Femi Falana SAN ya bayyana cewa zargin da shugaban kasar Amurkan ya yi na kisan Kiristoci a Najeriya, babu komai a cikinsa sai karya
  • Lauyan ya nuna cewa 'yan ta'addan da ke yin kashe-kashe a kasar nan babu ruwansu da tambayar addini idan suka tashi yin ta'addanci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babban lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya ragaragji shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Femi Falana ya ce Trump ya yi karya game da zargin cewa ana aiwatar da “kisan gillar Kiristoci” a Najeriya, yana mai cewa shugaban na Amurka ya raina kasashen Afirka.

Femi Falana ya soki Shugaba Donald Trump
Femi Falana da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: @Femifalana, @WhiteHouse
Source: Twitter

Babban lauyan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels TV a ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun tsara yadda za su kawo farmaki Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani Falana ya yi wa Trump?

Femi Falana ya ce zargin Trump cewa ana kashe dubban Kiristoci a Najeriya, babu wata hujjar da ta tabbatar da shi.

Ya bayyana cewa tashin hankalin da ake fuskanta a wasu yankuna na kasar nan ba ya da nasaba da addini, sai dai yana samuwa ne daga laifuffuka, rikici kan albarkatu da kuma satar mutane.

“Ra’ayina shi ne cewa Mista Trump ya yi wa duniya baki ɗaya karya kan zargin cewa ana kisan gillar Kiristoci a Najeriya ba tare da wata hujja ba."

- Femi Falana

“Ya ce wai an kashe Kiristoci 3,100 a Najeriya. Amma idan ka kwatanta wannan magana da gaskiyar abin da ke faruwa, za ka ga cewa masu kisan, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, barayin daji, ko ‘yan bindiga ba sa tambayar addininka."
"Abin da suke nema shi ne kuɗin fansa ko kuma abin da za su ci. Don haka, ba addini ke jawo hakan ba.”

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Ministan Tinubu, Keyamo ya tura budaddiyar wasika ga Shugaba Trump

- Femi Falana

Falana ya kara da cewa a jihohin da rikici ya daɗe kamar Benue da Plateau, tushen matsalar shi ne rikicin filayen noma da kiwo, ba sabanin addini ba.

“Masu kisa a can suna yin hakan ne domin su mallaki kasa ko kuma don su sami ciyawa ga dabbobinsu."

- Femi Falana

Femi Falana ya ce Trump ya yi wa Najeriya karya
Babban lauya a Najeriya, Femi Falana Hoto: @Femifalana
Source: Facebook

Falana ya ba gwamnati shawara

Babban lauyan ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina damuwa da maganganun Trump kan yiwuwar kai hare-hare a Najeriya, maimakon haka ta duba kura-kuranta a cikin gida wajen yaki da matsalar tsaro.

“Maimakon gwamnati ta damu kanta saboda maganar Trump, ya kamata ta tambayi kanta: a ina muka yi kuskure?"

- Femi Falana

Afenifere ta gano shirin Trump kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta taso Donald Trump a gaba kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Kungiyar ta bayyana cewa Trump ya yi barazanar don tilastawa Shugaba Bola Tinubu sayen makamai daga wajen Amurka.

Kara karanta wannan

Nijar da wasu kasashen Afrika 5 da Amurka ke da sansanin sojoji a cikinsu

Hakazalika, ta musanta zargin cewa ana zaluntar Kiristoci tare da yi musu kisan karr dangi a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng