Sakon Tinubu ga 'Yan Najeriya a kan Barazanar Donald Trump

Sakon Tinubu ga 'Yan Najeriya a kan Barazanar Donald Trump

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su kwantar da hankulansu kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan
  • Ministan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce shugaban ƙasa na tattaunawa da ƙasashen duniya don kare martabar Najeriya
  • Gwamnati ta ce fara daukar wadansu matakai don inganta tsaro a ƙasa bayan kalaman Donald Trump na cewa ana kisan kiristoci zalla

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ‘yan Najeriya su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa bayan barazanar da Donald Trump ya yiwa kasar.

Shugaban kasan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa tana aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan.

Gwamnati ta ce tana nazarin kalaman Donald Trump
Hoton Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngalela
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka bayan ganawa da shugaban ƙasa a fadar gwamnati, Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta sa labule da gwamnatin tarayya kan barazanar Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya

Ministan yada labaran ya ce gwamnatin Bola Tinubu na bin dukkannin matakan da suka dace don tabbatar da cewa Najeriya ta samu ingantaccen tsaro.

A kalaman Mohammaed Idris:

“Mun tattauna kan barazanar da Donald Trump ya yi wa ƙasarmu, kuma shugaban ƙasa yana nazarin lamarin a cikin natsuwa. Yana kuma ƙoƙarin sanar da ƙasashen duniya irin kokarin da Najeriya ke yi wajen magance matsalolin tsaro."

Ministan ya ce sauya shugabannin tsaro da shugaban ƙasa ya yi a ‘yan makonnin da suka gabata na cikin matakan da ake ɗauka don samar ingantaccen tsaro.

Gwamnati ta musanta zargin wariyar addini

Mohammed Idris ya yi watsi da zarge-zargen da wasu kasashen waje ke yi cewa Najeriya tana nuna bambanci wajen addini.

Najeriya ta ce kalaman Trump karya ne
Hoton Shugaban Amurka, Donald J Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Ya bayyana cewa tsarin mulkin ƙasa ya bai wa kowa cikakken ‘yancin yin addini da bin ra’ayinsa ba tare da tsangwama ba.

Kara karanta wannan

"Najeriya ba ta da damar goyon bayan kisan addini": Minista ya karyata Trump a idon duniya

Ya bayyana cewa:

“Bayyana Najeriya da ƙasar da ba ta girmama addini ba ba gaskiya ba ne. Kundin tsarin mulkinmu ya tanadi ‘yancin addini ga kowa."

Ya ƙara da cewa shugaba Tinubu yana nazarin duk bayanan da suka shafi wannan batu da hankali, kuma yana tabbatar da cewa lamura za su daidaita a hankali.

Mohammed Idris ya ce shugaban ƙasa na son ganin an samar da tsaro mai dorewa, wanda zai bai wa ‘yan ƙasa damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.

'Yan majalisar Amurka sun soki Trump

A baya, mun wallafa cewa ’yan majalisar wakilai daga Amurka, Gregory W. Meeks da Sara Jacobs, sun soki matakin Donald Trump na barazanar yiwuwar kai hari na soja.

Suna ganin wannan mataki ba abu ne mai kyau ba, musamman idan aka yi la’akari da cewa rikice-rikicen da Najeriya ke fuskanta ba su samu asali daga addini kawai ba.

Sun bayyana cewa sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake damuwa da su ta fuskar ‘yancin addini (CPC) ba zai warware matsalolin tsaro ba kuma zai iya jawo rabuwar kan yan kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng