Majalisar Dattawa Ta Kaddamar da Bincike kan Wasu Ayyukan da Buhari Ya Yi
- Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti na wucin gadi domin binciken ayyukan layin dogo da aka aiwatar a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Sanata Adams Oshiomhole ne ke shugabantar kwamitin da zai binciki hanyoyin samun kudi, kwangiloli, da matsalolin da suka shafi layin dogo na kasa
- Binciken ya biyo bayan lalacewar layin dogo na Itakpe–Warri fiye da sau 10 tun daga 2023 zuwa 2025, wanda ke jefa rayukan fasinjoji cikin hadari sosai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Majalisar Dattawan Najeriya ta kaddamar da bincike mai zurfi kan ayyukan layin dogo da aka aiwatar a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Majalisar za ta duba lamunin da aka karba, kwangilolin da aka bayar, da kuma yadda aka aiwatar da ayyukan.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa matakin ya zo ne bayan samun matsaloli da dama a kan layin dogo, musamman a Itakpe–Warri, inda aka samu matsaloli fiye da sau 10 a shekaru biyu da suka wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi karkashin jagorancin Sanata Adams Oshiomhole domin gudanar da cikakken bincike cikin mako hudu.
Dalilin fara binciken ayyukan Buhari
Sanata Ede Dafinone daga Delta ta Tsakiya da ya dauki nauyin kudirin, ya bayyana cewa binciken ya zama wajibi bayan matsalolin da ke faruwa a kan layin dogo na Itakpe–Warri.
Ya ce:
“Layin dogon da aka kaddamar ba da dadewa ba, yanzu yana fama da matsaloli da dama – daga karkacewar jiragen kasa zuwa lalacewar injuna – wanda ke barazana ga rayukan fasinjoji da kuma amincin jama’a.”
Dafinone ya kara da cewa irin wannan matsala a aikin da aka kashe makudan kudi wajen ginawa yana nuna bukatar duba yadda aka gudanar da shi daga farko har karshe.
Kalaman shugaban majalisar dattawa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya nuna rashin jin dadi kan yadda ayyukan aka gudanar a baya, yana mai cewa an nuna “rashin kwarewa da yaudara” wajen kula da ayyukan.
A cewarsa, ba abin yarda ba ne a kashe tiriliyoyin Naira a kan layin dogon kuma a ce ya lalace bayan ’yan watanni da kaddamar da shi.
"Wannan abin kunya ne, ya yi kama da tsohon jirgin da aka sake wa fenti aka ce sabo ne.”
Akpabio ya ce majalisar za ta tabbatar da gano gaskiya da ladabtar da duk wanda aka samu da hannu a cikin aikata almundahana.
Majalisar ta umurci ma’aikatar sufuri da hukumar jiragen kasa (NRC) da su gaggauta gyara layin dogon Itakpe–Warri da kuma daukar matakai don inganta tsaro da amincin tafiyar jiragen kasa.
Haka kuma, an yanke shawarar gudanar da bincike kan dukkan ayyukan layin dogo da aka aiwatar a karkashin gwamnatin Buhari, ciki har da:
- Kudin da aka yi amfani da su
- Yadda aka bayar da kwangiloli
- Ka’idojin da aka bi wajen yin layin dogon
Trump: An yi sabani a majalisar dattawa
A wani labarin, mun kawo muku cewa an samu sabani tsakanin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpbio da mataimakinsa, Barau Jibrin.
Shugabannin sun yi sabani kan tattauna ikirarin da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi game da zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
Barau Jibrin ya nuna yana so a tattauna maganar Donald Trump amma Akpabio ya nuna kin amincewa da bukatar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


