Ido Zai Raina Fata: An Cafke Ɗan Takarar NNPP da Zargin Kai wa Gwamna Bago Hari

Ido Zai Raina Fata: An Cafke Ɗan Takarar NNPP da Zargin Kai wa Gwamna Bago Hari

  • Rundunar ’yan sandan Jihar Niger ta yi babban kamu bayan wasu miyagu sun kai hari kan ayarin motocin gwamna
  • Jami'an sun kama mutane huɗu da ake zargi da kai hari kan gungun motocin a karshen mako da ya gabata lokacin da ake zaɓe
  • Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake gudanar da zaben ƙananan hukumomi a jihar wanda jam'iyyar APC ta yi nasara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Rundunar ’yan sandan Niger ta tabbatar da kama mutane huɗu dangane da harin da aka kai kan gungun motocin gwamnan jihar.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an farmaki ayarin motocin Gwamna Mohammed Umaru Bago a garin Bida a makon da ya gabata.

Matasa sun kai hari kan ayarin motocin Gwamna Bago
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Niger a Minna. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

An kama mutane saboda kai wa gwamna hari

Kara karanta wannan

Jira ya kare: Hukumar NSIEC ta fitar da sakamakon zaben kananan hukumomin Neja

Hakan na cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya fitar ranar Talata 4 ga watan Nuwambar 2025, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasiu Abiodun ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 2 ga Nuwamba, 2025 da karfe 1:45 na rana a Bida da ke jihar.

Ya ce harin ya faru ne lokacin da ayarin motocin gwamnan ke barin Bida zuwa Minna bayan kammala zaben kananan hukumomi a jihar.

“Rahotanni daga sashen 'B' na Bida sun nuna cewa wasu barayi da ’yan daba sun kai hari ga motocin gwamna da duwatsu da sauran makamai."

- Cewar sanarwar

An kama wasu da ake zargin sun farmaki Gwamna Bago
Gwamna Umaru Bago da Kwamishinan yan sanda a Niger. Hoto: Nigeria Police Force Niger State Command.
Source: Facebook

Barnar da hari kan Gwamna Bago ya jawo

SP Abiodun ya bayyana cewa jami'an yan sanda na sashen A da B na Bida sun gaggauta tura jami’ansu, inda suka yi amfani da hayaki mai saka hawaye don tarwatsa su.

Duk da haka, wasu motocin cikin gungun sun lalace yayin harin wanda hakan ya sa rundunar yan sanda suka bi wadanda suka kai harin don kama su.

Ya ƙara da cewa an kama mutane uku nan take, wato Ali Mohammed da Adamu Hussain na unguwar Nasarafu, da kuma Isah Umaru na Darachita.

Kara karanta wannan

Kama dalibin jami'ar da ya soki gwamna a Facebook ya fara tayar da kura a jihar Neja

'Dan takarar NNPP a zaben ya shiga hannu

Daily Trust ta ce an kama dan takarar shugaban ƙaramar hukuma na jam’iyyar NNPP a zaɓen da aka kammala a Jihar Neja, Abdulmalik Usman Nagenu.

An cafke Nagenu ne bisa zargin yana da hannu a harin da aka kai wa tawagar Gwamna Mohammed Umaru Bago.

Rahotanni sun ce an cafke Nagenu ne bayan wani bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta, inda aka jiyo wasu mutane da ba a tantance ba suna tattaunawa kan yadda suka shiga cikin harin.

Wasiu Abiodun ya ce:

“A wajen cigaba da bincike, an kama wani Abdulmalik Usman Nagemu mai shekaru 39 daga unguwar Bello Masaba, Bida."

Niger: Wasu daga cikin wadanda aka cafke

Jami'in ya ce binciken farko ya kai ga gano sunayen wasu mutane biyu, Salihu Mohammed da Abdulrahman Baba, kuma ana ci gaba da farautar sauran mutanen.

“Dukkan wadanda aka kama suna taimakawa bincike. Rundunar na ƙoƙari don kama sauran wadanda suka tsere."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kusan N5bn don wasu muhimman ayyuka

- Abiodun ya tabbatar

Niger: APC ya lashe zaben kananan hukumomi

Mun ba ku labarin cewa hukumar zaben Niger ta ce jam'iyyar APC ta lashe duka kujerun ciyamomi a kananan hukumomi 25 da ke jihar.

APC mai mulki ta kuma samu nasaran lashe kujerun kansiloli 271 daga cikin 274 yayin da PDP ta ci kujeru biyu kacal.

Hukumar NSIEC ta taya daukacin zababbun shugabannin murna tare da fatan za su gudanar da mulki bisa adalci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.