'Ba Na Jin Tsoron Trump,' An Samu Sabani tsakanin Barau da Akpabio a Majalisa

'Ba Na Jin Tsoron Trump,' An Samu Sabani tsakanin Barau da Akpabio a Majalisa

  • An samu hatsaniya a zauren majalisa yayin da mataimakin shugaban majalisar, Jibrin Barau, ya kalubalanci Godswill Akpabio
  • Sabanin ya biyo bayan maganganun shugaban kasar Amurka, Donald Trump, da ya zargi Najeriya da kisan gilla kan Kiristoci
  • Akpabio ya ce majalisar ba za ta ce uffan ba sai gwamnati ta turo da takarda, amma Barau ya dage cewa ba ya jin tsoron Trump

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An samu fada-in-fada a zauren majalisar dattawa a ranar Talata tsakanin shugaban majalisa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau Jibrin.

Sabanin ya tashi ne lokacin da Sanata Akpabio, ya ce majalisar ba za ta yi martani kan zargin da Donald Trump ya yi wa Najeriya ba har sai gwamnatin tarayya ta ba da cikakken bayani.

Kara karanta wannan

Tinubu zai karbo rancen sama da Naira tiriliyan 1, ya aika bukata ga majalisa

An samu sabani tsakanin Barau da Akpabio kan kalaman Trump
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Sanata Jibrin Barau. Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Kalaman Akpabio da suka fusata Barau

Jaridar daily Trust ta rahoto shugaban majalisar dattawan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wane ne ni da zan mayar wa Trump martani? Ba aikinmu bane mu yi magana kan abu da gwamnati ba ta kawo mana ba.”

Ya kuma ƙara da cewa:

“’Yan Najeriya na son mu faɗi ra’ayinmu, amma dole mu jira sakon gwamnati a hukumance kafin mu ɗauki matsaya.”

Sai dai maganar Akpabio ta fusata mataimakin shugaban majalisar, Jibrin Barau, wanda ya ce shi zai yi magana ba tare da jin tsoron kowa ba.

'Ba na tsoron Trump' - Barau ga Akpabio

Cikin zafin magana, Barau ya yi martani ga Akpabio, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Najeriya da Amurka: Abdulsalami Abubakar ya fadi me ya ke ganin shi ne mafita

“Ni na na tsoron Trump. Zan faɗi ra’ayina. Ni ɗan Najeriya ne, kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa na ƙasa mai cikakken 'yancin kai. Ba zan yi shiru ba idan ana zagin ƙasata."

Ya ƙara da cewa:

“Trump yana yada ƙarya game da ƙasarmu, kuma muna da ’yancin mu karyata shi. Kada ka wani ya ji tsoron fadar abin.”

Da yake mayar da martani ga Barau, Akpabio ya ce:

“Ni ban ce ina jin tsoro ba. Ta yaya shugaban majalisar dattawa zai ji tsoron Trump? Amma dai a guji maganar da mutane za su yi mata wata iriyar fassara ta daban.”

Akpabio ya umurci a goge maganar Barau

A yayin da muhawarar ke ci gaba, Akpabio ya juya zuwa ga magatakardan majalisa inda ya ba da umarnin a goge maganganun Barau daga kundin rahoton zaman.

Ya bayyana cewa Barau ya “yi maganar da ta saba wa tsarin zaman,” don haka maganarsa ba za ta shiga cikin kundin majalisa ba, in ji rahoton Business Day.

Kara karanta wannan

Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Sai dai Barau bai damu ba, inda aka ga ya tashi ya nufi kujerar Akpabio, sannan suka yi 'yar tattaunawa a asirce, lamarin da ya jawo hankalin sauran sanatoci kafin ya koma kujerarsa.

An samu 'yar hatsaniya a majalisar dattawa tsakanin Akpabio da Barau
Zauren majalisar dattawa yayin da sanatoci ke gudanar da zamansu a Abuja. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Abin da ya haddasa hayaniya a majalisar

Rigimar ta samo asali ne daga martanin Trump wanda ya zargi gwamnatin Najeriya da kisan Kiristoci da kuma tauye ’yancin addini, kamar yadda muka ruwaito.

Akpabio ya dage cewa majalisar ba ta da ikon yin magana kan irin wannan batu har sai an samu takarda daga fadar shugaban ƙasa.

Sai dai wasu sanatoci, ciki har da Barau, na ganin cewa majalisa tana da ikon kare mutuncin ƙasa idan wani shugaba daga waje ya yi kokarin bata sunan Najeriya.

Shirin Trump na kawo hari Najeriya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Donald Trump, ya yi barazanar cewa Amurka na iya turo sojojinta Najeriya ko kuma su kai hari ta sama domin hana “kisan kare dangi kan Kiristoci.”

A cikin sakon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump ya zargi “’yan ta’adda masu jihadi' da laifin “kashe Kiristoci,” yana mai cewa Kiristanci na fuskantar barazana a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Abin da dole Trump ya yi kafin kawo hari Najeriya": Hadimin Tinubu ya yi bayani

Duk da cewa Trump ya yi ikirarin cewa ana kashe Kiristoci, masana sun bayyana cewa yawancin wadanda ake kashewa Musulmai ne a yankin Arewacin ƙasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com