Yanayin da 'Yan Najeriya Suka Shiga yayin da Farashin Kayan Abinci Ya Sauka
- Faduwar farashin kayan abinci a fadin Najeriya ya kawo sauƙin rayuwa ga iyalai da ke fama da matsin tattalin arziki
- Rahotanni sun nuna cewa farashin kayan abinci ya ragu da kusan kashi 30 saboda wasu matakai da gwamnati ta dauka
- Masu sayayya da iyalai da dama sun bayyana farin ciki da fatan farashin kayan abinci zai ci gaba da raguwa a kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rahoto ya nuna cewa farashin kayan abinci a Najeriya ya ragu sosai a watannin da suka gabata.
Lamarin ya kawo sauƙin rayuwa ga mutane da dama bayan dogon lokaci na fama da hauhawar farashi.

Source: Getty Images
Binciken jaridar Business Day a manyan birane ya nuna cewa farashin kayan masarufi ya sauka da kusan kashi 30 idan aka kwatanta da bara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda farashi ya sauka a Najeriya
A birnin Legas, rahoto ya nuna cewa buhun shinkafar gida mai nauyin kilo 50 ta gida ta dawo N65,000, daga N73,000 a watan Oktoba 2024, an samu ragin kashi 11.
A daya bangaren kuma, shinkafar waje ta sauka daga N82,000 zuwa N62,000, raguwar da ta kai kashi 24.
A bangaren kayan gwari, farashin kwandon tumatir ya ragu daga N50,000 zuwa N35,000, raguwar kashi 30.

Source: Getty Images
A Abuja kuwa, buhun shinkafar gida da ake sayarwa N75,000 a bara , yanzu ya koma N63,000, an samu saukin kashi 16.
A kasuwar Abuja, ƙaramar kwandon shinkafa (mudu) yanzu ya koma N2,500 daga N5,000 da ake sayarwa a baya.
Martanin 'yan Najeriya kan saukar farashi
Wata ma’aikaciyar lafiya a Legas, Ogechi Chimereme ta bayyana farin cikinta da wannan sauyi, tana cewa:
“Na je kasuwa kwanan nan, sai na ji daɗi da yanayin farashi. Na saye kaya fiye da yadda na tsara saboda sun yi sauƙi.”
Ta ce kafin wannan sauƙin, ta kan ƙara kasafin abincin gidanta saboda tsadar kayan masarufi a kasuwanni.
Wata mai sayar da kayan marmari a Berger, Legas, mai suna Esther Ejiro, ta bayyana fatan cewa farashin kayan abinci zai ci gaba da raguwa.
“Na yi matuƙar farin ciki. Ina fatan wannan yanayi zai dore,”
- Inji ta
Dalilin saukar farashin kaya a Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa a shekarar 2024, Najeriya ta fuskanci tsadar abinci mai tsanani, inda hauhawar farashin abinci ta kai kashi 40.87 a watan Yuni.
Amma a watan Satumba 2025, Daily Trust ta kawo rahotanni daga hukumar kididdiga da suka nuna cewa hauhawar farashin abinci ya ragu sosai.
Kamfanin binciken zuba jari na Cardinal Stone ya bayyana cewa raguwar hauhawar farashi ya samo asali ne daga faduwar farashin abinci da kuma ingantuwar tsaro.
Majalisa na son rage shigo da shinkafa
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta fara muhawara kan neman rage shigo da shinkafa Najeriya.
Wasu 'yan majalisa sun bayyana cewa matakin zai taimaka wajen kara tsaron abinci da habaka tattalin arzikin Najeriya.
Kungiyoyin masu casar shinkafa a Najeriya sun yaba da yunkurin da majalisar ta fara domin a cewarsu, hakan zai kawo cigaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


