Martanin Shugaban Sojojin Najeriya kan Ikirarin Yi wa Kiristoci Kisan Kare Dangi

Martanin Shugaban Sojojin Najeriya kan Ikirarin Yi wa Kiristoci Kisan Kare Dangi

  • Hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede ya yi martani kan zargin kisan kare dangi ga Kiristoci da kasar Amurka ta yi
  • Ya ce rundunar soji na ci gaba da aiki tukuru domin dakile ta’addanci da tabbatar da tsaron a fadin Najeriya
  • Janar Oluyede ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta dauki matakan karfafa tsaro, da sabunta tsarin rundunar tsaron kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa babu kisan kare dangi ko wariya da ake cewa ana yi wa Kiristoci a Najeriya.

Yayin da ya yi martani, Janar Oluyede ya ce babban kalubale da kasar ke fuskanta a halin yanzu shi ne ta’addanci.

Janar Olufemi Oluyede
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Punch ta ce ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja, inda ya mayar da martani kan ikirarin da shugaban Amurka Donald Trump.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ana dar dar a Najeriya, malami ya tabbatar da kisan Kiristoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Oluyede ya bayyana cewa irin wadannan kalamai na iya jefa kasar cikin rudani, saboda haka ya bukaci kasashen duniya su fahimci cewa matsalar Najeriya ba ta addini bace.

Kokarin dakile ta'addanci a Najeriya

A cewar hafsan tsaron, rundunar sojin Najeriya tana aiki tukuru domin tabbatar da tsaro da kuma rage ta’addanci a sassa daban-daban na kasar.

Ya ce sababbin tsare-tsare da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar cikin ‘yan kwanakin nan suna taimakawa wajen karfafa ayyukan tsaro.

“Shugaban kasa wanda shi ne kwamandan rundunar soji ya sake tsara tsarin tsaron kasar ta hanyar kawo jami’ai masu gaskiya da kwarewa domin karfafa ayyukanmu,”

- Inji shi

Karin matakan yaki da ta’addanci

Janar Oluyede ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa rundunar tsaro za ta kara himma wajen yaki da ta’addanci da sauran miyagun laifuffuka a fadin kasar.

Shugaba Tinubu, Donald Trump
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce za a kara karfin aiki da dabaru domin tabbatar da an dakile duk wani yunkurin ta’addanci a cikin Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi taron habaka noma da rage shigo da kayan abinci daga waje zuwa Najeriya

“Za mu kara kuzari da dabaru a ayyukanmu don tabbatar da cewa mun dakile ta’addanci a cikin kasar nan,”

Inji hafsan tsaron Najeriya

'Ta’addanci matsalar duniya ce,' Oluyede

Janar Oluyede ya kara da cewa ba Najeriya ce kadai ke fama da ta’addanci ba, ya ce matsala ce da ta shafi kasashe da dama a duniya.

The Nation ta rahoto ya bayyana cewa akwai bukatar hadin kai tsakanin kasa da kasa domin shawo kan matsalar.

Ya ce:

“Kasashe da dama suna fama da irin wannan kalubale, saboda haka ya zama dole mu hada kai da su domin magance ta’addanci cikin hadin gwiwa,”

Hafsan tsaron ya sake jaddada kudirin rundunar soji na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin Najeriya.

Abdulsalam ya yi wa Trump martani

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar ya yi martani kan barazanar Donald Trump ga Najeriya.

Tsohon shugaban ya ce barazanar tana da hadari ga hadin kan kasa lura da halin da Najeriya ke ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

CAN: Martanin Kiristocin Arewa bisa barazanar Trump na kawo farmaki a Najeriya

Janar Abdulsalam ya bukaci Najeriya da Amurka su zauna a tebur domin shawo kan sabanin da aka samu cikin lumana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng