Akpabio: Natasha Ta Fusata bayan Jami'ai Sun Kwace Mata Fasfo a Filin Jirgi
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce jami’an shige da ficen Najeriya sun kwace mata fasfo a filin jirgi, sun hana ta fita ƙasar waje
- Ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da bayar da umarnin hana ta tafiya saboda zargin tana jawo wa Najeriya abin kunya
- Sanata Natasha da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta bayyana haka ne kwanaki kadan bayan ta gayyaci Akpabio da 'yan majalisa zuwa jihar Kogi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta bayyana cewa jami’an hukumar shige da fice ta kasa (NIS) sun kwace mata fasfo.
Ta bayyana haka ne a safiyar ranar Talata, 4 ga watan Nuwamba, 2025 inda ta ce jami'an suna yunkurin hana ta fita kasar waje domin ta yi hutu.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro ya gargadi Trump bayan barazanar kawo hari Najeriya, Buratai ya bada mafita

Source: Facebook
A bidiyon wanda ta wallafa kai tsaye a shafinta na Facebook, Sanata Natasha ta bayyana cewa ba ta san abin da ta yi ba da har za a rika hana ta fita kasar waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Natasha ta ce an kwace mata fasfo
A cewar Natasha, bayan ta kammala bikin cika shekaru biyu da zama a majalisar dattawa, inda ta kaddamar da wasu ayyuka a mazabarta, sai ta yi yunkurin zuwa hutu kasar waje.
Ta bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka kwace mata fasfo bisa umarnin Shugaban Majalisar Dattawan ba.

Source: Facebook
A kalamanta:
“Ina nan a filin jirgi, an hana ni fasfona. Ba ni da wani laifi, babu kuma umarnin kotu da ke hana ni tafiya."
Natasha ta ce jami’in da ya tsayar da ita ya bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya bayar da umarnin a hana ta fita ƙasar waje.

Kara karanta wannan
Amurka ta gindayawa Najeriya sharadi bayan barazanar kawo hari kan zargin kisan kiristoci
Ta ce a cewar jami'in, Shugaban Majalisa ya bada umarnin ne saboda yana zargin tana “ɓata sunan ƙasa” a kafafen labarai na duniya.
Natasha ta zargi Akpabio da karya doka
Sanatar ta bayyana abin da ya faru a matsayin take haƙƙinta na ‘yancin tafiya da kuma tauye dokar ƙasa.
Natasha ta ce a lokacin da irin wannan lamari ya faru da ita a baya, sai bayan wani mutum mai tasiri ya sa baki ne aka dawo mata da fasfon nata.
A cewarta, wannan karon ma Akpabio ne ya bayar da sabon umarni ga shugaban hukumar shige da fice da a hana ta fita ƙasar.
Ta kuma bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya riga ya umarci Babban Lauyan Gwamnati, Lateef Fagbemi, da a janye duk shari’o’in da gwamnatin tarayya ta shigar kanta.
A ƙarshe, jami’an hukumar sun dawo mata da fasfon nata bayan tattaunawa ta ciki a lokacin da ta ke daukar bidiyo kai tsaye.
Dalilin Natasha na gayyatar Akpabio zuwa Kogi
A baya, mun wallafa cewa Sanata Natasha Akpoti‑Uduaghan, wacce ke wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ta bayyana dalilin da ya sa ta gayyaci Godswill Akpabio zuwa Kogi.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi wa Trump martani mai zafi kan zargin kashe Kiristoci, ta ce karya ne
Ta kara da cewa wannan mataki na gayyata wani bangare ne na nuna girmamawa ga tsarin majalisar da dokokin ƙasa, kuma ba shi da nasaba da siyasa ko nuna kishin kai.
Sanata Natasha ta koma bakin aiki bayan an dakatar da ita tsawon watanni shida saboda dambarwarta da Akpabio, inda ta fara shiga ayyukan majalisa da gabatar da kudirori.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng