Tashin Hankali: An Kama Bindigogi da Mugayen Makamai Ana Shirin Shiga da Su Zamfara
- Dakarun rundunar kare al'umma da gwamnatin Zamfara ta dauka (CPG) sun samu nasara a kokarinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama'a
- Ankarawan Zamfara sun kama wata mota dauke da makamai ciki har da bindigogi kirar AK47 da ake zaton na yan bindiga ne
- Direban motar da aka kama dauke da makaman ya ce bai san komai ba, yana mai cewa wata mata ce ta dora kayan daga tashar Gusau
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Jami'an tsaro na rundunar Community Protection Guard (CPG) wadanda gwamnatin Zamfara ta kirkiro domin yakar matsalar tsaro sun kama makamai.

Kara karanta wannan
Kama dalibin jami'ar da ya soki gwamna a Facebook ya fara tayar da kura a jihar Neja
Dakarun CPG da aka fi sani da Askarawan Zamfara sun cafke mugayen makamai da suka hada da bindigogi da alburusai, wadanda ake kyautata zaton za a shiga da su jihar domin kai wa yan bindiga.

Source: Original
Rahoton Leadership ya nuna cewa dakarun tsaron sun kama makaman ne a cikin wata mota lokacin da suke aikin binciken ababen hawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ankarawa sun kama makamai a Zamfara
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa daga cikin makaman da jami'an tsaron suka gano a cikin motar akwai bindigogi biyu kirar AK-47, RPG ɗaya, da kuma wasu alburusai da dama.
Wani jami’in rundunar tsaro ta CPG da ya bayyana sunansa da Salisu Adamu, ya ce sun kama motar ne a lokacin da suke gudanar da binciken tsaro na yau da kullum a kauyen Dangulbi.
“An ɓoye makaman ne a cikin kwalaye da aka cika da kifi ta yadda ba za a yi zargin da wani abu daban a ciki ba.
"Lokacin da muka nemi mu bincika motar, direban ya fara nuna ba sai an yi hakan ba amma muka dage, sai muka gano abin da ke cikin wadannan kwalaye” in ji Adamu.
Yadda direban mota ya dauko makamai
Direban motar da jami'an CPG suka kama, Bashar Mustapha, ya tabbatar da cewa an samu wadannan mugayen makamao ne a motarsa, amma ya yi ikirarin cewa ba nasa bane.
A cewarsa, ya ɗauko fasinjoji da kaya ne daga wata tasha ta Gusau zuwa Magami, kafin jami’an CPG su tare shi a daidai kauyen Dangulbi, cewar rahoton Daily Post.
“Makaman na cikin wawu kaya ne da wata mata ta ɗora daga Gusau. Ni ban san abin da take ɗauke da shi ba,” in ji Mustapha.

Source: Facebook
Rahotanni sun ce an mika motar tare da makaman da aka kama ga hukumomin tsaro domin ci gaba da bincike.
Gwamnan Zamfara ya yi gargardi kan sulhu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi gargadi kan hawa teburin sulhu da ake yi da 'yan bindiga ba tare da sun ajiye makamai ba.
Gwamna Dauda ya yi gargadin cewa sulhun da ke barin kungiyoyin ‘yan bindiga da makaman su tare da ba su damar sa sharudda, ba zai magance tashin hankalin da ake ciki ba.
Ya ce abubuwan da ke faruwa a Zamfara, suna nuna irin kalubalen da ake fuskanta a sassa da dama na Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya wajen neman zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

