Najeriya da Amurka: Abdulsalami Abubakar Ya Fadi me Ya ke Ganin Shi ne Mafita

Najeriya da Amurka: Abdulsalami Abubakar Ya Fadi me Ya ke Ganin Shi ne Mafita

  • Tsohon shugaban ƙasa Janar Abdulsalami Abubakar ya bukaci Donald Trump da ya goyi bayan Najeriya a maimakon yin barazana
  • Hakan na zuwa ne bayan Trump ya saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da cin zarafin Kiristoci tare da barazanar kai hari
  • Abdulsalami ya yi gargadin cewa irin waɗannan kalamai da ba a tabbatar da su ba na iya haifar da barazana ga ɗorewar haɗin kan ƙasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar ya roƙi shugaban Amurka Donald Trump da ya tallafa wa Najeriya wajen yaƙi da matsalar tsaro maimakon ya rika fitar da barazana.

Abdulsalami ya bayyana hakan ne a cikin wata hira ta wayar tarho da aka yi da shi daga London, inda ya nuna damuwa kan yadda maganganun Trump za su iya jefa haɗin kan Najeriya cikin haɗari.

Kara karanta wannan

"Zan goyi bayan Trump": Wike ya yi magana kan barazanar shugaban Amurka

Janar Abdulsalam, Bola Tinubu
Abdussalam Abubakar yayin ganawa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Wani rahoton The Cable ya ce Abdulsalami ya yi kira da a yi amfani da hikima da diflomasiyya wajen magance wannan rikici na kalmomi tsakanin ƙasashen biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganganun Donald Trump kan Najeriya

A ranar Juma’ar da ta gabata, Donald Trump ya sanar da cewa ya sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke karkashin CPC bisa zargin ana kisan kiyashi ga Kiristoci.

Trump ya kuma yi gargaɗi ga gwamnatin Najeriya da ta “gaggauta daukar mataki” ko kuma zai cika barazanar da ya yi ta dakatar da duk wani taimako da tallafin Amurka ke bai wa Najeriya.

Baya ga haka, ya ƙara da cewa zai tura ma’aikatar yaƙin Amurka don yaƙar “'yan ta’addan da ke kai hare-hare kan Kiristocinmu masu daraja.”

Kiran Abdulsalami ga Amurka da Najeriya

A nasa martanin, Janar Abdulsalami ya bayyana cewa kalaman Trump “barazana ne mai tsanani ga haɗin kan Najeriya da aka samu bayan wahalhalu.”

Kara karanta wannan

Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Ya bukaci Amurka da ta rungumi hanyar taimako da tattaunawa maimakon barazana, yana mai cewa hakan ne zai ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Donald J Trump
Shugaban Amurka, Donald J Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abdulsalami ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su “a ji tsoron Allah, su haɗa kai don kare mulkin ƙasa da zaman lafiya.”

Ya ce ya kamata hadin kai, hikima da diflomasiyya su fi rarrabuwa da girman kai a wannan lokaci mai muhimmanci.

Abdulsalami ya nemi tattaunawa da Trump

Janar Abdulsalami ya ƙara da cewa akwai buƙatar a zauna teburin tattaunawa da Trump domin warware batutuwan da suka taso cikin natsuwa da dabaru.

A cewarsa, tattaunawa tsakanin shugabannin biyu za ta taimaka wajen rage zafin kalmomi da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu.

Abdulsalami Abubakar ya mulki Najeriya na dan lokaci kafin ya mika mulki ga farar hula.

Martanin fadar shugaban kasa ga Trump

A wani labarin, mun kawo muku cewa Fadar shugaban ƙasa ta Najeriya ta ce zai yiwu Bola Ahmed Tinubu da Trump su gana domin tattauna batun zargin kisan Kiristoci.

Fadar shugaban ƙasa ta ce wannan ganawa za ta zama dama ta fayyace matsayar Najeriya da kuma tabbatar da cewa ba a nuna bambancin addini a ƙasar.

Kara karanta wannan

'Ta sama ko ta kasa,' Donald Trump ya fadi shirinsa kan kai hare hare Najeriya

Sai dai ba a fayyace lokacin ganawar ba, kuma hadimin shugaban kasa ya karyata cewa Bola Tinubu zai tafi Amurka ranar Talata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng