"Abin da Dole Trump Ya Yi kafin Kawo Hari Najeriya': Hadimin Tinubu Ya Yi Bayani

"Abin da Dole Trump Ya Yi kafin Kawo Hari Najeriya': Hadimin Tinubu Ya Yi Bayani

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kawo hari kan Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci
  • Hadimin Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa kuskure ne a dauki irin wannan matakin ba tare da amincewar gwamnati ba
  • Daniel Bwala ya kuma musanta zargin cewa ana tsangwamar Kiristoci tare da yi musu kiran gilla a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya yi martani kan barazanar Shugaba Donald Trump ta kawo hari Najeriya.

Daniel Bwala ya ce sabawa diflomasiyya ne idan Amurka ta aiwatar wani matakin soja a Najeriya ba tare da cikakkiyar amincewar gwamnatin tarayya ba.

Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Donald Trump
Source: Twitter

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne wata tattaunawa da BBC World Service a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Martanin wasu manyan Arewa kan barazanar Trump ta kai farmaki Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Tinubu ya jaddada cewa Najeriya kasa ce mai cikakken ‘yancin gashin kai, kuma duk wani shiri na taimako kan harkokin tsaro dole ne ya kasance na haɗin gwiwa da kuma girmama ikon kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Najeriya a matsayin “kasa mai babbar matsala” saboda zargin tsangwamar Kiristoci.

Me hadimin Tinubu ya ce kan Trump?

Da yake martani, Bwala ya ce kalaman Trump an fassara su ta hanyar da ba daidai ba, yana mai nuna tabbacin cewa za a fayyace batun ne lokacin da Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Ya kuma yaba wa Trump saboda amincewa da sayar da makamai ga Najeriya a wa’adin mulkinsa na farko.

Bwala ya yi watsi da zargin cewa ana gudanar da kisan gilla kan Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa rashin tsaro na shafar ‘yan kasa ne gaba ɗaya ba tare da la’akari da addini ba.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya shawarci Tinubu ya tattaro tsofaffin shugabannin kasa kan barazanar Trump

“Muna godiya ga Shugaba Donald Trump saboda a wa’adinsa na farko ya amince da sayar da makamai da suka taimaka wa Najeriya wajen ƙarfafa yaki da ta’addanci."
“A wa’adinsa na biyu ma, ya sake nuna sha’awar tallafa wa yaƙi da Boko Haram, wanda muna maraba da shi, amma irin wannan taimako dole ya dogara ne da sahihan bayanan leken asiri, ba kan jita-jita ko labaran kafafen sada zumunta ba.”

- Daniel Bwala

Bwala ya nuna kuskuren barazanar Trump

Dangane da barazanar Trump na yiwuwar kai hari, Bwala ya jaddada cewa irin wannan mataki zai halatta ne kawai idan an gudanar da shi tare da gwamnatin Najeriya.

Bwala ya yi martani kan barazanar Trump
Daniel Bwala tare da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @BwalaDaniel
Source: Twitter
“Idan hadin gwiwa ce da Najeriya, wannan ya dace. Amma ta fuskar diflomasiyya, kuskure ne a mamaye kasa mai ‘yancin kai ba tare da haɗin gwiwa ba."
"Musamman kasa kamar Najeriya da ke taka muhimmiyar rawa wajen yakar rashin tsaro."
“Ana ɗaukar irin wannan mataki ne kawai idan an tabbatar cewa gwamnati tana da hannu a cikin rikici, wanda ba haka lamarin yake ba a Najeriya."

- Daniel Bwala

Malamin addini ya gano shirin Trump

Kara karanta wannan

'Kamar Libya, Iraq,' Sowore ya fadi hadarin zuwan sojojin Amurka Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya yi magana kan barazanar da Donald Trump, ya yi wa Najeriya.

Primate Ayodele ya yi ja kunnen Shugaba Tinubu da ya zama cikin shiri saboda zargin kisan Kiristoci da Amurka ke yadawa.

Malamin addinin ya ce wannan duk shirin adawa ne da ake yi don a kawar da Tinubu daga mulki kafin 2027 ko kuma a lokacin zaɓe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng