Kwana Ya Kare: Gwamna Abba Ya Yi Jimami da Allah Ya Yi Wa Durbin Kano Rasuwa
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin rasuwar Durbin Kano, Muhammad Lawan Koguna, wanda ya amsa kiran Mahaliccinsa a ranar Juma'a
- Abba ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da sauran jama'ar jihar Kano bisa wannan rashi, inda ya yi addu'ar Allah Ya gafarata masa
- Gwamnan Kano ya ce rasuwar Durbin Kano babban rashi ne ga kasa baki daya, wanda ya bar gibin da zai wahala a iya cikewa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi jimami game da rasuwar Marigayi Durbin Kano, Muhammad Lawan Koguna.
Durbin Kano, Alhaji Muhammad Koguna ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma’a da ta gabata, 31 ga watan Oktoba, 2025 bayan doguwar jinya.

Source: Facebook
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar ta’aziyya da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya yi alhinin rasuwar Durbin Kano
Gwamna Yusuf ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai juriya da jajircewa, wanda rayuwarsa ta kasance abin koyi na aiki tukuru da sadaukarwa.
Ya ce gudummawar da Marigayi Muhammad Koguna ya bayar wajen ci gaban Jihar Kano ba za a taɓa mantawa da ita ba.
“Yau muna jimamin rasuwar ɗan Kano na gari mai koshi, babban ɗan kasuwa kuma mai riƙe da muƙamin gargajiya, Marigayi Durbin Kano, Muhammad Lawan Koguna.
"Rasuwar Muhammad Koguna babban rashi ne ga jihar Kano da ƙasa baki ɗaya,” in ji Gwamna Abba.
Gwamna Abba ya fadi alherin marigayin
Gwamna Abba ya kara da cewa marigayin ya rasu ne a daidai lokacin da jihar Kano ke bukatar mutum irinsa.
A sanarwar, Gwamna Abba ya ce:
"Durbin Kano ya bar duniya a lokacin da mu ke matuƙar buƙatar irin kokari gudummuwarsa, ba iyalansa kadai suka yi rashi ba, har ma da jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan
"Nan gaba za ku gode mini," Gwamma Diri ya fadi asalin dalilin ficewarsa daga PDP
"Mun rasa ginshiƙi mai karfi da kwarin gwiwa, rashin Muhammad Koguna ya bar gibi mai wahalar cikewa.”
Gwamnatin Kano ta mika sakon ta'aziyya
A madadin Gwamnatin Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, majalisar masarautar Kano da kuma al’ummar jihar baki ɗaya bisa wannan babban rashi.

Source: Facebook
Ya roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jikansa da rahama, Ya kuma bai wa iyalansa haƙuri da ƙarfin zuciya na don jure wannan babban rashi, in ji Daily Trust.
"Ina rokon Allah SWT Ya garfa masa kura-kuransa, Ya jikansa da rahama Ya sa shi a gidan Aljannatul Firdausi. Muna rokon Allah ba iyalansa hakuri," in ji shi.
Mahaifiyar tsohon gwamna ta rasu
A wani rahoton, kun ji cewa mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmad Adamu Mu'azu ta riga mu gidan gaskiya a karshen makon da ya gabata.
Gwamna Bala Mohammed ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya yi alhinin wannan rashi tare da yi wa marigayiyar addu'o'in neman gafara.
Gwamnan ya bayyana halayen marigayiyyar na kirki da suka hada da bautar Allah da zikiri, sada zumunci da kuma son jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

