Barazanar Trump: Nuhu Ribadu Ya Sa Labule da Sababbin Hafsoshin Tsaro
- Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya kira manyan hafsoshin tsaro domin ganawa da su
- Nuhu Ribadu ya shiga ganawa hafsoshin tsaron tare da wasu shugabannin hukumomin tsaro da leken asiri a birnin tarayya Abuja
- Ganawar tasu dai na zuwa ne bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar daukar matakin soja kan Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya shiga ganawa da manyan hafsoshin tsaro.
Nuhu Ribadu na yin ganawar ne da hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro da leken asiri na Najeriya.

Source: Twitter
Ribadu ya gana da hafsoshin tsaro
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Nuhu Ribadu da manyan hafsoshin tsaro sun shiga ganawar ne a babban birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da ake kammala wannan rahoto, ba a bayyana ajandar wannan ganawa ba.
Jaridar Vanguard ta ce ana sa ran bayan kammala taron, Nuhu Ribadu zai yi bayani ga manema labarai kan halin da ake ciki.
Trump ya yi barazana ga Najeriya
Wannan taron ya biyo bayan rahotannin da suka bayyana cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya umarci a fara shiri don yiwuwar ɗaukar matakin soja a Najeriya.
Donald Trump ya yi barazanar tura sojojin Amurka zuwa Najeriya idan ba a dakatar da abin da ya kira kisan gillar Kiristoci ba.
A wani rubutu da ya fitar a dandalinsa na Truth Social ranar Asabar, Trump ya umurci ma'aikatar tsaron Amurka da ta fara shiri don yiwuwar daukar mataki idan kisan ya ci gaba.
Ya kuma yi gargaɗin cewa Amurka za ta dakatar da duk wani taimako da take bai wa Najeriya idan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kasa kawo karshen abin da ya kira tsangwama da kisan Kiristoci.
"Idan har gwamnatin Najeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk taimako ga Najeriya nan take."
"Kuma watakila za mu shiga cikin wannan kasar da yanzu ta wulakanta da makamai, don kawar da 'yan ta'addan Musulmai da ke aikata irin wadannan mummunan laifuffuka."
- Donald Trump

Source: Twitter
Gwamnati za ta yi wa 'yan Najeriya jawabi
Tun da farko shugaban hukumar wayar da kan jama’a (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya ce mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da manyan hafsoshi za su yi magana da manema labarai kan barazanar da Shugaban Amurka ya yi.
A cewarsa, taron na manema labarai zai bai wa gwamnati damar bayar da gamsashshiyar amsa kan zargin kisan gillar da bayyanawa jama’a kokarin da ake yi na dakile rashin tsaro da sauran miyagun al’amura.
Shehu Sani ya ragargaji Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi wa shugaban Amurka, Donald Trump, martani kan kiran Najeriya wulakantacciyar kasa.
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa Najeriya ba wulakantacciyar kasa ba ce kuma ba za ta taba zama hakan ba.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya
Tsohon sanatan ya yi watsi da barazanar Trump ta kawo farmaki a Najeriya saboda zargin zaluntar Kiristoci da yi musu kisan gilla.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

