Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Bindiga a Kano, an Samu Asarar Rayuka
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi fafatawa mai zafi da wasu 'yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari a jihar Kano
- 'Yan bindigan dai sun yi yunkurin kai hare-haren ne a wasu kauyuka na karamar hukumar Shanono domin tafka barna
- Sai dai, dakarun sojoji sun yi artabu da su, wanda ya jawo aka kashe kusan guda 10 daga cikinsu tare da kwato babura
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation MESA, karkashin Brigade ta 3 ta rundunar sojojin Najeriya, sun dakile wani harin 'yan bindiga a jihar Kano.
Dakarun sojojin sun dakile harin ne wanda ‘yan bindiga suka kai kan wasu kauyuka a karamar hukumar Shanono, jihar Kano, inda suka kashe ‘yan ta’adda 19.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar, Babatunde Zubairu, ya fitar.

Kara karanta wannan
Kano: 'Yan bindiga sun hallaka mutane bayan sace da dama, an 'gano' inda suka fito
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka ragargaji 'yan bindiga
Dakarun tare da taimakon wasu hukumomin tsaro, sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan, bayan samun bayanan sirri kan motsinsu a yankunan Ungwan Tudu, Ungwan Tsamiya, da Goron Dutse da misalin karfe 5:00 na yamma a ranar 1 ga Nuwamba, 2025.
A cikin sanarwar, ya bayyana cewa dakarun sojoji sun hanzarta zuwa wurin tare da tarwatsa ‘yan bindigan da ke kan babura, lamarin da ya jawo doguwar musayar wuta.
“A lokacin artabun, an hallaka ‘yan bindiga 19, sannan an kwato babura da dama da kuma wayoyi guda biyu."
- Kyaftin Babatunde Zubairu
Sai dai, rundunar ta tabbatar da cewa sojoji biyu da ɗan sa-kai guda ɗaya sun rasa rayukansu a yayin artabun.
Kyaftin Zubairu ya ce ana ci gaba da gudanar da karin ayyukan tsaro a yankin domin kare al’ummomin da ke cikin haɗarin farmaki da kuma hana satar shanu da sauran laifuffuka.
Sojoji sun ba jama'a shawara a Kano
Rundunar sojojin Najeriya ta bukaci jama’a da su ci gaba da zama masu lura, tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani abin da suka gani da ba su yarda da shi ba.

Source: Original
Kwamandan Brigade ta 3, Brigediya Janar Ahmed Tukur, ya tabbatar wa jama’a masu bin doka cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kano, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Sojojin sun bayyana wannan aikin a matsayin bangare na yunkurin da ake ci gaba da yi domin tabbatar da tsaro a yankunan karkara da dawo da kwarin gwiwar jama’a a wuraren da ‘yan bindiga ke kai hare-hare.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar ragargazar 'yan bindiga a jihar Kebbi.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga kusan 100 yayin artabun da suka yi da su a karamar hukumar Ngaski.
Hakazalika, sojojin sun kwato babura tare da kubutar da mutanen da 'yan bindigan suka sace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

