Barazanar Kawo Hari: Shehu Sani Ya Yi Wa Trump Martani Mai Zafi

Barazanar Kawo Hari: Shehu Sani Ya Yi Wa Trump Martani Mai Zafi

  • Ana ci gaba muhawara kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump, ya yi na kawo farmaki a Najeriya
  • Shugaba Donald Trump ya yi barazanar kawo farmakin saboda zargin muzgunawa Kiristoci tare da kashe su
  • Sai dai, Sanata Shehu Sani, ya fito ya yi wa Trump wankin babban bargo kan yadda ya saki baki ya yi kalamai marasa kyau

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, tsohon sanata, ya yi martani kan barazanar Donald, ta kawo farmaki a Najeriya.

Sanata Shehu Sani wanda ba bakon tota albarkacin bakinsa ba ne, ya nuna kin amincewarsa kan shigowar kowace irin rundunar ketare a Najeriya.

Shehu Sani ya yi wa Donald Trump martani
Sanata Shehu Sani da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: @ShehuSani, @WhiteHouse
Source: Twitter

Tsohon sanatan ya yi martanin ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba 2023.

Kara karanta wannan

Martanin wasu manyan Arewa kan barazanar Trump ta kai farmaki Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soja a Najeriya kan zargin tsangwamar da ake yi wa Kiristoci.

Hakazalika ya kuma bayyana Najeriya a matsayin “wulakantacciyar kasa”.

Wane martani Shehu Sani ya yi wa Trump?

A martanin da ya yi, Shehu Sani ya ce Najeriya ba za ta taɓa zama “wulakantacciyar kasa ba".

Har ila yau ya ja hankalin cewa mutane masu zuwa nan gana za su tambayi matsayar kowane mutum a irin waɗannan lokuta.

“Wata rana dukkanmu za mu tafi mu bar duniya. ‘Ya’ya da zuriyar mu za su karanta abin da muka rubuta a wannan lokaci, kuma za su tambayi, wace matsaya muka dauka kan manyan batutuwan da suka ɗaga hankali a wannan zamaninmu?”
“Ni ina son tarihi ya rubuta ni a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka nuna adawa, suka ƙaryata, kuma suka yi Allah wadai ba tare da wata shakka ba da kowane irin farmakin soja da Mr. Trump zai iya yi wa kasata a kowace hanya ko dalili.”

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro ya gargadi Trump bayan barazanar kawo hari Najeriya, Buratai ya bada mafita

“Kasata ba ta zama ‘wulakantacciyar kasa' ba kuma ba za ta taɓa zama ba. Duk wanda yake alfahari da mahaifiyarsa wacce ta haife shi bayan nakuda a kasarsa ta asali, ba zai yarda a kira kasarsa ‘wulakantacciya’ ba.”

- Sanata Shehu Sani

Shehu Sani ya aika sako ga Amurka

Hakazalika, tsohon sanatan ya nemi gwamnatin Amurka ta kalli kanta a madubi.

“Ba mu taɓa kasancewa kasa da ta yi mulkin mallaka, bautar da mutane ko mamaye wata kasa da bama-bamai da kashe miliyoyin mutane ba, ko kwashe albarkatun su ba."
"Tun da ba mu da wannan tarihin na aikata irin wadannan abubuwan ga wasu kasashe, ba zai yi wa a kira mu 'wulakantattu ba'."

- Sanata Shehu Sani

Shehu Sani ya yi watsi da barazanar Trump
Sanata Shehu Sani wanda ya taba wakiltar Kaduna ta Tsakiya Hoto: @ShehuSani
Source: Twitter

Shehu Sani ya aminta cewa kasar nan tana fuskantar matsalolin tsaro a cikin shekaru 15 da suka gabata, amma ya ce:

“Muna maraba da duk wani taimako da zai taimaka wa rundunonin tsaron mu wajen murkushe da halaka ‘yan ta’adda a kasarmu.”

A karshe, ya yi kira ga gwamnati da ta kara himma wajen kare rayukan jama’a da tabbatar da tsaro a kasa, wadda a cewarsa, ita ce kasar da ba ta bukatar biza don mu zauna a cikin ta.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya shawarci Tinubu ya tattaro tsofaffin shugabannin kasa kan barazanar Trump

“A matsayina na mai kishin dimokuraɗiyya, ina girmama ra’ayoyin wasu, amma ba zan taɓa goyon bayan ra’ayin waɗanda ke goyon bayan kawo farmaki daga ketare ba. Bari tarihi ya rubuta su a matsayin masu goyon bayan hakan."

- Sanata Shehu Sani

Janar Buratai ya gargadi Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon babban hafsan sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya yi magana kan barazanar shugaban Amurka, Donald Trump.

Buratai ya shawarci Donald Trump da ya janye barazanar da ya yi ta kawo farmaki a Najeriya kan zargin kisan Kiristoci.

Tsohon babban hafsan sojojin bayyana cewa abin da zai kawo sauki shi ne kasar ta rungumi hanyar hadin kai maimakon amfani da karfi a dangantakarta da Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng