Trump: Da Gaske Tinubu zai Tafi Amurka ba Shiri? Fadar Shugabansa Ta Magantu

Trump: Da Gaske Tinubu zai Tafi Amurka ba Shiri? Fadar Shugabansa Ta Magantu

  • Fadar shugaban kasa ta musanta labarin cewa Bola Tinubu zai ziyarci Amurka domin ganawa da mataimakin shugaba Donald Trump
  • Hadimin shugaba Bola Tinubu, Temitope Ajayi, ya bayyana rahoton a matsayin karya da ya haddasa rade-radi a kafafen sada zumunta
  • Ya ce idan Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyara Fadar White House, to zai gana ne da Shugaba Donald Trump, ba da mataimakinsa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja — Fadar shugaban kasa ta yi watsi da wani rahoto da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tafi Amurka a ranar Talata domin ganawa da mataimakin Donald Trump, J.D. Vance.

Rahoton wanda ya samo asali daga wata kafar labarai, ya jawo ce-ce-ku-ce da rade-radi a tsakanin ‘yan Najeriya da masu sharhi kan harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

'Kamar Libya, Iraq,' Sowore ya fadi hadarin zuwan sojojin Amurka Najeriya

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Sai dai, a sakon da hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Temitope Ajayi, ya wallafa a X, ya ce babu wata tafiya da aka tsara, kuma labarin karya ne maras tushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ba zai je Amurka ba

Ajayi, cikin wani rubutu da ya wallafa a ranar Litinin, Ajayi ya bayyana cewa labarin zuwan Tinubu Amurka na bogi ne, wanda wasu suka yi amfani da shi wajen yada jita-jita maras tushe.

Punch ta rahoto ya ce:

“Akwai wani labarin Sahara Reporters da ke cewa Shugaba Tinubu zai tafi Amurka a ranar Talata domin ganawa da mataimakin shugaban kasa, J.D. Vance.
"Wannan labarin ba gaskiya ba ne. Idan shugaba Tinubu zai kai ziyara fadar White House, ba zai je wajen mataimakin shugaban kasa ba.”

Ajayi ya kara da cewa irin wadannan labarai na bogi suna iya haifar da rudani a tsakanin jama’a da kuma bata sunan gwamnati.

Kara karanta wannan

Yadda ta kaya tsakanin Buhari da Trump a fadar White House kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Tushen jita-jitar da martanin gwamnati

Rahoton bogin ya biyo bayan wata magana ne da hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya yi kan haduwar Tinubu da Trump.

An fara cewa zai kai ziyarar ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya da barazanar kai farmaki da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi.

Donald J Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Trump, a wani sako da ya ftar a ranar Asabar, ya yi barazanar cewa Amurka za ta “kai farmaki da bindigogi” idan gwamnatin Najeriya ba ta dakatar da kashe Kirista ba.

Ya ce:

“Idan gwamnatin Najeriya ta ci gaba da barin kashe kirista, Amurka za ta dakatar da duk wani taimako.
"Kuma za mu iya shiga kasar nan kai tsaye domin murkushe ‘yan ta’addan.”

Martanin shugaba Tinubu ga Trump

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya kasa ce mai bin tsarin dimokuradiyya da ke tabbatar da ‘yancin addini da daidaito tsakanin kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya

Ya ce gwamnatin sa tana ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai, Musulmai da Kiristoci, domin tabbatar da zaman lafiya da kawo karshen matsalolin tsaro.

Shugaban kasar ya jaddada cewa tsarin mulkin Najeriya yana tabbatar da ‘yancin addini ga kowa, kuma gwamnati za ta ci gaba da kare wannan hakki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng