Gwamnatin Kano Ta Ware kusan N5bn don Wasu Muhimman Ayyuka

Gwamnatin Kano Ta Ware kusan N5bn don Wasu Muhimman Ayyuka

  • Gwamnatin Kano ta amince da kashe sama da Naira biliyan 4.9 domin gudanar da ayyuka daban-daban na bunkasa ilimi
  • Ayyukan sun haɗa da gyaran makarantu, samar da kayan koyarwa, da inganta cibiyoyin karatu a fadin kananan hukumomin Kano
  • Da yake jawabi a kan dalilan kashe wadannan kudi, Abba Kabir Yusuf na ganin hanya ce ta inganta rayuwar jama'a a nan gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe sama da Naira biliyan 4.9 don gudanar da manyan ayyuka da nufin farfado da harkar ilimi a fadin jihar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan bindiga sun hallaka mutane bayan sace da dama, an 'gano' inda suka fito

Gwamnatin Kano ta fitar da N4.9n a kan ilimi
Hoton gwamna Abba Kabir Yusuf tare da wasu daliban Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A sakon da Sanusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce majalisar zartarwa ta jihar ta amince da kudin ne yayin zaman ta na 33 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Abba na warewa makarantu kudi

A cewar sanarwar, wadannan ayyuka za su taimaka wajen inganta gine-ginen makarantu, karfafa matakin koyarwa da koyo, da kuma bai wa yara da matasa damar samun ilimi mai inganci.

Daga cikin abubuwan da aka amince da su akwai gyaran Makarantar Gwamnati ta Fasaha da ke Ungogo da biyan bashin masu samar da abinci a makarantun kwana.

Abba Kabir Yusuf ya amince a yi aiki a bangaren ilimi
Hoton Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamnatin ta kuma amince da samar da kayan koyarwa da karatu ta hanyar Kamfanin Buga Littattafai na Kano.

Haka kuma za a kammala da samar da kayayyakin dakunan karatu na zamani a Kwalejin Ilimi na Kano, da kuma aikin tantancewa da sahalewa a Jami’ar Fasaha ta Kano.

Kara karanta wannan

Kotu ta jikawa PDP aiki, ta dakatar da babban taron jam'iyyar na kasa

Haka kuma, an amince da kudin sayen kayan ofis a Jami’ar North West, domin inganta gudanar da harkokin karatu da gudanarwa.

Abba ya jaddada aniyarsa ta cigaban Kano

A cikin sanarwar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf yana nan a kan kudirinsa na ciyar da jihar Kano gaba da samar da ayyukan raya kasa da jama'a.

Ya bayyana cewa:

“Ilimi shi ne ginshiƙin shirin ci gabanmu, kuma za mu ci gaba da zuba jari wajen samar da kayan aiki da wuraren da za su inganta koyarwa da karatu."

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin cike gibin da aka samu a tsarin ilimi a Kano.

Sannan ana kokarin tabbatar da cewa kowace yarinya da yaro a Kano na da damar zuwa makaranta cikin yanayi mai inganci da tsaro.

Gwamna Abba ya magantu kan rashin tsaro

A baya, mun wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin ƙarfafa tsaro a kan iyakokin Kano saboda hare-haren 'yan bindiga da aka fara samu a sassan jihar.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani bayan Tinubu ya sassauta hukuncin Maryam Sanda

Umarnin ya biyo bayan wasu hare-haren ‘yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar mutane uku a kananan hukumomin ‎Shanono da ‎Tsanyawa a cikin 'yan kwanakin da suka wuce.

Wata sanarwa da kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Lahadi, gwamnan ya ce hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’umma ne mabuɗin dakile irin waɗannan matsaloli.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng