Juyin Mulki: Mutanen da Sojoji Suka Kama a Gidan Tsohon Gwamna na Ta Shan Matsa

Juyin Mulki: Mutanen da Sojoji Suka Kama a Gidan Tsohon Gwamna na Ta Shan Matsa

  • Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu jami'an tsaro na tsare da mutanen da aka kama daga gidan tsohon Ministan Timipre Sylva a Abuja
  • Rundunar tsaro ta kai samame gidan tsohon ministan man fetur, wanda ya yi gwamna a Bayelsa, bisa zarginsa da hannu a yunkurin juyin mulki
  • Jami'an tsaron sun yi awon gaba tare da kama kaninsa da direbansa, kuma har yanzu suna tsare a hannun hukuma suna shan matsala

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu jami’an tsaro suna binciken wasu mutane biyu da aka kama daga gidan tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva.

Jami'an sun kai samame gidan tsohon ministan man fetur na tarayya, Timipre Sylva, a ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025 saboda zargin yunkurin juyin mulki.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda sojojin da aka tsare suka 'tona asirin' tsohon minista, Timipre Sylva

Ana cigaba da bincike a kan zargin juyin mulki
Shugaban kasa, Bola Tinubu tare da Hafsoshin tsaro Hoto: @Sundaydare
Source: Twitter

Jaridar Punch ya tabbatar da cewa jami'an sun kama kanin tsohon Ministan mai suna Paga da direbansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka dura a gidan tsohon minista

Rahoton ya ce tsohon gwamna Timipre Sylva baya gida ba lokacin da abin ya faru, domin yana ƙasar waje, kuma ya ki dawowa har yanzu.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Facebook

Majiyoyi sun bayyana cewa ya dakatar da dawowarsa Najeriya ne bayan jin cewa an kama wasu da ake zargin suna shirin juyin mulki.

Julius Bokoru, mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya musanta cewa Sylva yana da alaƙa da wani shirin juyin mulki.

A cewarsa, wasu ‘yan siyasa ne ke ƙoƙarin bata masa suna saboda suna ganin shi barazana ne ga burinsu a nan gaba.

Sojoji na tsare da 'dan uwa, diraban Sylva

A wata hira da manema labarai, Bokoru ya tabbatar cewa mutanen biyu da aka kama har yanzu suna tsare.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi matsalar sulhu da 'yan bindiga, ya yi gargadi

Ya ce:

“Da sun sake su, da na sani. Har daren jiya suna hannun jami’an tsaro.”

A wani bangare, masu ruwa da tsaki a yankin Neja-Delta sun gargadi masu yada batanci kan shugaban hukumar raya yankin kuma tsohon hadimin Sylva, Dr. Samuel Ogbuku.

Kungiyar Critical Ex-agitators Stakeholders Coalition ta fitar da sanarwa bayan wani taro a birnin Fatakwal inda ta yi kira ga shugabannin gargajiya da na siyasa su marawa Ogbuku baya.

Mai magana da yawun kungiyar, Nature Kieghe, ya yaba wa Ogbuku saboda yadda yake tafiyar da ayyukan ci gaba, musamman shirin “Light Up Niger Delta.”

Ya kuma bayyana cewa hukumar NDDC ta kammala ayyuka sama da 300 a cikin kwata na uku na 2024 tare da rage ayyukan 'yan ta'adda a yankin.

Ana zargin shirin juyin mulki

A baya, mun wallafa cewa wasu majiyoyi sun tabbatar cewa tsohon gwamna daga Kudancin Najeriya yana fuskantar bincike bisa zargin cewa yana da hannu a shirin juyin mulki.

Kara karanta wannan

Shirin juyin mulki: Sojoji sun bi diddigin N45bn zuwa hukumar raya Neja Delta

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kama sojoji 16 da ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da wani Birgediya Janar daga Jihar Neja da wani Kanal daga Nasarawa.

Duk da wandannan zarge-zarge, rundunar sojin Najeriya tare da gwamnatin kasar sun karyata cewa akwai batun yunkuri na juyin mulki a kasar, tare da cewa an tsare sojoji n ne saboda aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng